Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya taya al’ummar musulmai a jihar da ma duniya baki daya murna bisa bikin babbar sallar Layya ta wannan shekarar.
A sakon fatan alkairi da gwamnan ya fitar ta hannun kakakinsa, Ismaila Uba Misilli, ya nuna cewa, lokacin bikin Idi babba, lokaci ne na koyi da sadaukarwa, kyauta da rabon ababen bukata ga marasa shi.
- Saraki Ga Gwamnonin APC: Ba Za Ku Iya Kwace Wa PDP Wike Ba
- Kungiyar Huffazul Kur’an Ta Bai Wa Almajirai 80 Tallafin Sana’a A Neja
Ya kuma bukaci jama’a da su yi koyi da irin sadaukarwa da sallamawar Annabi Ibrahim na soyayyya, kauna, hadin kai da kyautata wa makusanta.
Ya kuma nemi da a yi wa jihar addu’ar neman tabbatuwar zaman lafiya da karin ci gaban ababen more rayuwa, sannan ya nemi Musulmai da su yi amfani da wannan lokacin wajen yin addu’a ga kasar nan domin samun nasarar dakile matsalolin tsaro da sauran matsalolin da suka shafi al’ummar da kasa.
Gwamna Inuwa ya yi amfani da damar wajen jinjina wa irin gudunmawar da sarakunan jihar ke bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali hadi da ci gaban jihar a kowane lokaci.
Inuwa ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su tabbatar sun mallaki katin zabe domin samu damar zabar wadanda suke so a 2023.
Ya bada tabbacin azamar gwamnatinsa wajen tabbatar da ci gaba da samar da ababen more rayuwa da ribar demokuradiyya ga al’ummar a kowane lokaci.
Daga karshe ya yi addu’ar Allah sa a yi bukukuwan wannan sallar cikin koshin lafiya.