Gwamna Bala Muhammad na Jihar Bauchi, ya nuna bukatar da ke akwai ga jama’a da su rungumi dabi’ar yafiya, sadaukarwa, gami da mutunta juna.
Ya nuna bukatar da ke akwai na cewa a dukufa addu’ar zaman lafiya da neman Allah ya sauko da wadataccen ruwan sama domin manoma su samu dimbin amfanin gona a daminar bana.
- Chelsea Ta Sayi Sterling Daga Manchester City
- Saraki Ga Gwamnonin APC: Ba Za Ku Iya Kwace Wa PDP Wike BaÂ
A jawabinsa na fatan alkairi domin bikin babbar sallar Layya da kakakinsa Malam Mukhtar Gidado ya fitar ga al’umma, Bala ya yi tilawar cewa, Alkur’ani Mai girma ya nemi al’ummar musulmai da suke sadaka daga cikin arzikin da Allah ya musu ga mabuka ya ba tare da nuna bangaranci ba.
Don haka ne ya tunatar da al’ummar muhimmanci sadaka musamman a irin wannan lokacin na Layya.
Ya ce, ana Layya ne domin sadaukar, don haka ne ya nemi jama’a a kowani lokaci suke sallamawa wa umarnin Allah da kyautata niyya wajen gudanar da lamuran ayyuwarsu.
Ya kuma nemi masu hannu da shuni da suke sadaka ga wadanda suke cikin halin rashin babu.
Bala Muhammad sai ya bada tabbacin gwamnatinsa na ci gaba da lalubo hanyoyin da za su kyautata rayuwar al’umma, yana mai neman jama’a da su ci gaba da musu addu’o’in fatan alkairi.
Bala ya yi amfani da damar wajen tababtar da cewa gwamnatinsa ta gudanar da ayyukan raya jihar Bauchi masu dimbin yawa, kuma a shirye suke su ci gaba da hakan ba tare da gajiyawa ba.
A daidai lokacin da ke taya al’ummar murna, ya kuma yi fatan za a gudanar da dukkanin bukukuwan wannan sallar cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali.