Rahotanni sun bayyana cewar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, ya amince da daukar Musulmi a matsayin wanda zai masa takarar mataimaki a zaben 2023.
Wata majiya mai karfi a Kungiyar Yakin Neman Zaben Tinubu, wacce ta bukaci a sakaya sunanta, ta tabbatar wa da Kamfanin Dillacin Labarai (NAN) hakan a yau Lahadi a Abuja.
- Buhari Ya Jinjina Wa Masu NYSC Kan Gyara Rijiyoyin Burtsatse A Daura
- Fasinjoji 16 Sun Bace Sakamakon Nutsewar Kwale-kwale A Legas
Majiyar ta shaida wa NAN cewa Tinubu zai bayyana sunan mataimakin takararsa a makon da za a shiga.
A baya-bayan nan, an yi ta muhawara a kasa kan addinin ‘yan takarar shugaban kasa da abokan takararsu.
Sai dai kuma Tinubu ya dauki Kabiru Ibrahim Masari daga jihar Katsina a matsayin wanda zai masa mataimaki na wucin gadi.
Yin takarar Musulmi biyu a matsayin shugaba da mataimaki ya tada kura, musamman a yankin kudancin Nijeriya wanda suke ganin hakan kamar rashin adalci ne ga nasu yankin da kuma addinin.