Hukumar Kula da gidajen gyaran hali ta Nijeriya (NCoS) ta ce, akalla fursunoni 53, 836 a gidajen gyaran hali 253 ne ake tsare da su a fadin kasar nan suna dakon jiran shari’a a lissafin da ke kasa a ranar 18,ga Disambar 2023.
Mai magana da yawun hukumar, Mataimakin Kwanturola (ACC) Abubakar Umar ne ya shaida wa manema Labarai a Abuja ranar Alhamis.
- Hukumar Da Ke Kula Da Gidajen Yarin Nijeriya Na Cigiyar Fursunoni 69 Da Suka Tsere Daga Kuje
- Gwamnatin Tarayya Na Kashe Miliyan 3 Kullum Wajen Ciyar da Fursunoni 4,000 – Minista
Umar ya ce, takaita fursunoni a fadin kasar nan ta hanyar yanke musu hukunci da kuma wadanda ke jiran tuhuma sun kai 77,849.
A cewarsa, jimillar fursunoni 24, 013 “ya kara da cewa fursunonin maza da aka yankewa hukuncin sun kai 23,569 da mata 444.
“Kididdigar ta nuna cewa kashi 69 cikin 100 na fursunonin da ake tsare da su a gidajen gyaren hali da ake tsare da su suna jiran shari’a, yayin da kashi 31 cikin 100 na fursunonin aka yanke musu hukunci,” in ji shi.
Umar ya ce daya daga cikin kalubalen da hukumar ke fuskanta shi ne batun rugujewar gine-ginen da ke haifar da cunkoso a cikin gidajen gyaren halin da ke kasar nan.
Ya ce, kwanan nan gwamnati ta gina ƙarin wuraren ajiya na zamani guda 3,000 a shiyyoyin Nijeriya shida don rage cunkoso a gidajen gyaren halin da ake da su.
Ya ce, shirin zai taimaka wajen rage cunkoso a cibiyoyin tare da inganta walwala da lafiyar fursunonin.
“An kaddamar da na Kano kuma muna sa ran kammalawa cikin gaggawa da sanya sauran kayayyakin da ake bukata,” in ji shi.
Ya kara da cewa “aikin da ake yi na Abuja da da Portharcourt ana dab da kammalawa kuma nan ba da jimawa ba za a kaddamar da su.”
Ya kuma yabawa Gwamnatin Tarayya kan tara naira miliyanN585 don biyan tarar fursunoni a wani yunkuri na rage cinkoso a gidajen gyaran hali da ke a fadin kasar nan.
Ya kuma yaba da kokarin gwamnatin tarayya na sakin fursunoni 4,068 da ke zaman gidan gyaren hali daban-daban a kasar nan.