A wani yunkuri na dakile hana yaran da ba sa zuwa makaranta da kuma inganta koyarwa, Shugaba Bola Tinubu ya sake bullo da shirin ciyar da dalibai a makarantu.
Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman ne, ya sanar da hakan a yayin wani taron kara wa juna sani kan inganta harkokin ilimi.
- Majalisar Dattijai Ta Amince Da Naɗin Alkalai 11 A Kotun Ƙoli Da Tinubu Ya Aike Da Su
- Fursunoni 53,836 Ke Jiran Shari’a Don Sanin Matsayinsu A Gidajen Gyaren Hali A Nijeriya
Shirin wanda a baya aka dakatar da shi a zamanin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, yanzu zai koma karkashin ma’aikatar ilimi, don samar da abinci mai gina jiki ga dalibai har ma da karfafa yara suke zuwa makaranta.
Shugaba Tinubu yana da yakinin shirin zai zaburar da yara suke zuwa makaranta tare da ba su damar samun ilimin da suke bukata a matakin farko.
Ministan ya jaddada cewa: “don gano yadda za a yi amfani da manufofin shirin don magance matsalolin daban-daban da ke hana dalibai zuwa makaranta.”
Ana sa ran dawowar shirin ciyar da makarantu zai magance kalubale da dama ga yaran da ba sa zuwa makaranta ke fuskanta da suka hada da yunwa, fatara, da rashin samun ilimi.
Ta hanyar samar da abinci da yanayin mai kyau, shirin zai iya karfafa dalibai suke zuwa makaranta.