Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi tsokaci kan watanni shida da gwamnatinsa ta yi a kan garagar mulki, inda ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa su tsammaci samun sakamako mai kyau daga cikakkun manufofinsa na sauye-sauye da ya aiwatar a shekara mai zuwa.
Ya kuma bakaci a bai wa gwamnatinsa goyon baya kan inganta harkokin tsaro a yankin kudu maso gabas da kudu maso kudu da arewa maso gabas da arewa maso yamma, inda ya ce jami’an tsaro na fatattakar ‘yan Boko Haram da ‘yan bindiga.
- Majalisar Dattijai Ta Amince Da Naɗin Alkalai 11 A Kotun Ƙoli Da Tinubu Ya Aike Da Su
- Kiran Minista Ga VON: Ku Yaɗa Kyawawan Labarun Nijeriya Ga Duniya
Shugaban ya bukaci hukumomin tsaro da su kara himma wajen ganin kasar nan ta kubuta daga ayyukan ta’addanci.
Tinubu ya yi wannan jawabi ne a lokacin da yake kaddamar da sabon rukunin runduna ta shiyyar Inugu na hukumar yaki da yi wa tattalin arziki tu’annati (EFCC) a Inugu.
Ya samu wakilcin mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, wanda shi tsohon shugaban hukumar yaki da yi wa tattalin arziki tu’annati ne.
Ya ce, “Da farko, ina kawo gaisuwar Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu. Ya ce ya kamata in taya shugaban EFCC, Ola Olukoyede da tawagarsa murna. Na gode da kyakkyawan aiki da kuke yi.
“Ya ce ya kamata in gode wa sojojin Nijeriya da jami’an tsaron ’yansanda da jami’an tsaro na farin kaya (DSS) da sauran su bisa irin kyakkyawan aiki da kuke yi a kasarmu a yau.
“Kowa zai yarda da ni idan na ce abubuwa suna canzawa. A cikin watanni shida na farkon wannan gwamnati, mun fara ganin abubuwan da zai yiwu. Muna kuma so mu kara muku kwarin kwiwa wajen ci gaba da bin wannan hanyar.
“Muna bukatar kasarmu ta yi aiki. Muna bukatar abubuwa don inganta tsarin. Muna son yin abubuwan da suka dace. Kuma shi mai girma shugaban kasa yana kan gaba wajen yin hakan. Al’amura suna canjawa a Nijeriya. A 2024, ku jira ku ga abin da zai faru.”
Ribadu ya tabbatar wa dukkan hukumomin tsaro kudirin shugaban kasa na ba da fifiko ga jin dadinsu, ya kuma yi kira gare su da su yi aiki tare domin samun sakamako mai kyau.