Bisa alkaluman da gwamnatin kasar Sin ta fitar a yau, yawan mutanen da suka rasu sakamakon girgizar kasa mai karfin maki 6.2 da ta auku a arewa maso yammacin kasar Sin, ya karu zuwa mutane 117 a lardin Gansu, inda adadin a Qinghai ya kai mutane 31.
Hukumar ba da umurnin gudanar da aikin ceto ta lardin Gansu, ta ce, ya zuwa karfe 8 na safiyar yau bisa agogon wurin, bala’in ya shafi mutane 781.
Wannan girgizar kasa ta auku ne a daren ranar Litinin, da misali karfe 12 saura minti 1, ta kuma kai zurfin kilomita 10 daga karkashin kasa. (Amina Xu)