Gwamnatin Jihar Filato, ta kaddamar da rabon takin zamani kimanin buhu 120,000 ga manoma 40,000, Domin kara bunkasa noman rani na bana.
Mataimakiyar Gwamnan Jihar Josephine Piyo ce, ta mika wannan takin zamani ga jami’in hukumar noma na jihar (FADAMA) da kuma na shirin PADP da shirin CARES, domin raba wa manoman da za su amfana da takin.
- Rikicin Siyasar Jihar Ribas:Â Dattawa Da Kabilar Ijaw Sun Yi Fatali Da Sabon Sulhu Bisa Zargin Kashin Dankali
- CAC Ta Bayyana Dalilan Da Ke Kawo Durkushewar Kamfanoni A Nijeriya
Piyo ta ce, gwamnatin jihar ta karbo takin ne daga shirin yaki da cutar Korona na gwamnatin tarayya. Sannan ta yi nuni da cewa, mika takin da ya kai kimanin sama da buhu 120,000, don raba wa manoman jihar, zai taimaka wajen rage yunwa a fadin jihar.
Kazalika ta bayyana cewa, a karkashin shirin na ‘NG+CARES’; wanda ake yin sa a jihar, ya hada da gina hanyoyi guda 25 a Kanannan Hukomin Jihra 17, musamman domin samun saukin yin safarar amfanin gona zuwa kasuwanni.
Jami’in shirin na ‘NG-CARES’ a jihar, wanda ya karbi kayan a madadin sauran manoman da suka amfana, Dakta Haggai Gutap ya bayyana cewa, za a raba wa manoman da za su amfana da takin don rage musu zafin radadin annobar Korona da ta taba bulla a kasar nan da kuma kokarin samar da wadataccen abinci a fadin kasar.
Ya kara da cewa, tabbas fannin aikin noma na samar da matsakaita da kuma kananan sana’oi, inda ya bayyana cewa; takin zai kuma taimaka wajen bunkasa rayuwar manoma da iyalansu da kuma habaka tattalin arzikin Nijeriya baki-daya.