A jiya Jumma’a 22 ga watan nan, mataimakiyar shugaban kamfanin Tesla na kasar Amurka Tao Lin, ta yi tsokaci da cewa, “Kasuwar kasar Sin tana da makoma mai haske da ta fi rinjaye, idan aka kwatanta da kasuwannin sauran kasashen duniya, don haka ya zama wajibi a kafa kamfanin kirar Tesla a Sin.” A jiyan ne kuma aka kaddamar da kamfanin kera batir na motar Tesla wato Megapack a yankin masana’antu na Lingang dake birnin Shanghai na kasar Sin, kamfanin da ya kasance irinsa na farko da Tesla ya kafa a wajen Amurka.
Tun farkon shekarar bana, kamfanonin da ‘yan kasuwan kasashen ketare suka kafa a kasar Sin kamar Tesla suna karuwa cikin sauri, lamarin da ya shaida cewa, ‘yan kasuwan ketare suna cike da imani kan kasuwar kasar Sin matuka.
- Gajiyar Da Sin Ta Samarwa Duniya Bayan Yin Gyare-Gyare Da Bude Kofa Ga Ketare
- Sin Ta Bayyana Matukar Adawa Ga Amurka Game Da Batun Sayarwa Taiwan Makamai
Kuma sabbin alkaluman da hukumar gwamnatin kasar Sin ta fitar a ranar 21 ga wata, sun nuna cewa, adadin sabbin kamfanonin da ‘yan kasuwan ketare suka kafa ta hanyar zuba jari kai tsaye a kasar Sin ya kai 48,078 a cikin watanni 11 na farkon shekarar bana, adadin da ya karu da kaso 36.2 bisa dari kan makamancin lokacin shekarar bara. Ana iya cewa, kasuwar kasar Sin tana jawo hankalin ‘yan kasuwan ketare sosai.
Hakika zuba jari a kasar Sin, yana nufin zuba jari kan damammaki, saboda kasar Sin tana da babbar kasuwa, da manyan gine-ginen more rayuwar al’umma masu inganci, da tsarin samar da kayayyaki bisa daidaito, da ci gaban kirkire-kirkire ba tare da rufa rufa ba, da muhallin cinikayya da ya kara kyautatuwa, da kuma isassun kwararrun da ake bukata, duk wadannan suna iya samar da tabbaci ga gudanarwar kamfanonin jarin waje, tare kuma da samar musu da riba mai tsoka.
Shin mene ne yake jawo hankalin ‘yan kasuwan ketare da su kafa kamfanoninsu a kasar Sin? Abu mafi muhimmanci shi ne tattalin arzikin kasar Sin yana ci gaba da rika matsayin ci gaba yadda ya kamata. (Mai fassara: Jamila)