Shafin da ke zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma. Tsokacinmu na yau zai yi duba ne dangane da abin da ya shafi zumunci, duba da yadda wasu mutanen ke mantawa da cewa; Sadar da zumunci wajibi ne ta hanyar sallama, gaisawa da kyauta, da taimako, zama tare da dan’uwa, da yi wa dan’uwa magana, da kyautatawa da dai sauransu.
Duk da cewa malamai na yawaita bayani kan ma’anar zumunci ko ‘yan’uwantaka tana da fadi, ba ta takaita ne kawai ga ‘yan’uwa na jini ko tsatso ba, har da abokan zama makusanta, da ‘yan’uwa na addini, da sirikai. Sai dai wasu na mantawa da falalar da ke cikin zumunci har su tabarbarar da ita, wanda sadar da ita na daga; 1, Dalilan amsa addu’a. 2, Allah na sanya albarka a gidajen da ake sada zumunci. 3, Dalili ne na tsawon rai. 4, Mai sadarwa danginsa za su so shi. 5, Tana sabbaba yalwar arziki. 6, Tana kusantarwa ga Aljanna da Nisantawa daga wuta. 7, Mai sadarwa na tare da taimakon Allah. 8, Zumunta za ta yi kyakkyawar shaida ga mai sadar da ita. Haka ma mai yanke ta ba zai shiga Aljanna ba, da dai sauransu.
Wannan ya sa shafin TASKIRA jin ta bakin wasu daga cikin ma’abota shafin game da wannan batu; Shin Mene ne zumunci?, Su wa ya kamata ayi zumunci da su?, Ko me yake janyo tabarbarewar zumunci?, Ko mene ne illar yankewar zumunci?.
   Ga dai bayanan nasu kamar haka:
Sunana Zainab Zeey Ilyas, Jihar Kaduna:
Zumunci shi ne; dangantaka ta haihuwa, uwa, da uba da ‘yan’uwa, da kaka da jikoki, da abin da yayi sama ko kasa, yin zumunci wajibi ne wanda kuma wasu su da kansu ke kokarin yanke shi, ta hanyar nuna rashin kulawa ga wanda yayi niyyar kyautata musu, ko ziyartarsu tare da basu wata kyauta, wanda a wajensu take abin kushewa ko kuma abar rainawa a wajensu, dalilin hakan na iya haifar da rashin kulawar gabadaya da har ma da rashin yin kyautar ga wanda ake son yi wa, misalu; maruka, ko kishiyar uwa, ko yayye, ko wasu ‘yan’uwa daga cikin dangi, ko wanda ake ‘ya’yan uba da su da dai sauransu.
Sunana Aliyu Idris Sarkin Yaki Malumma:
Mahimmancin zumunci na da yawa kwarai da gaske, da farko dai mun riga da mun sani cewa zumunci ba ra’ayi bane wajibi ne, Allah ta’ala ya yi umarni da sada zumunta, Suratul Bakra Ayah ta 36 da kuma Ayah ta 210, Suratul Nisa’I, sannan Suratul Isra’I Ayah ta 26, Suratul Rum Ayah ta 38, kadan daga cikin mahimmancin zumunci sune; sada zumunta na kara tsawon rai, yana kara Arziki, sada zumunta dalili ne na samun Aljannah sannan siffa ce ta muminai, sannan yana sanyawa a karbi ayyukan mutum, daga mahimmancin zumunci yana kara kawo hadin kai da soyayya tsakanin ‘yan uwa. ‘Yan uwa wadanda suke uwa daya uba daya, ‘yan uwa da suke uba daya, ‘yan uwa ‘ya’yan kanin mahaifi ko kanwar mahaifiya ko kuma yayyensu, ‘yan uwa wadanda suke dangi ko nace ahali ne na mahaifi ko mahaifiya. Abubuwan da ke kawo nakasu a zumunci sune kamar rashin kulawa, yawan jita-jita, zargi, daukar maganganu da ba su da tabbas, rashin kai ziyara ga ‘Yan uwa, rashin halarta idan aka gayyace ka, rashin yin alkhairi duk kankantarsa idan muka duba a da iyayenmu ko soson wanke-wanke za su aika wa ‘yar uwarsu domin kulawa. illar yankewar zumunci tana da yawa kwarai da gaske kuma a bayyane take, kadan daga ciki sune; zai kasance mutum zai rayu tamkar baida kowa baida dangi, sannan duk ‘yan uwa babu wanda zai halarci wani taro ko na suna ko biki idan ya taso mutane za su yi tsammanin mutum bai da dangi, sannan yana sanya mutum cikin wahala da rashin kwanciyar hankali babbar matsalar idan ciwo ya kama mutum wanda zai kasance an fi son ‘yan uwa kusa da shi zai kasance babu ‘yan uwan da za su kula domin jinya mummunan abu kuma shi ne bayan mutuwar mutum zai bar iyalinsa ko iyalinta cikin yanayi na rashin shakikai masu kulawa dasu, sannan kuma ga alhaki ranar gobe kiyama. Shawara ita ce aji tsoron Allah ta’ala kasancewar Allahu (SWT) da kansa shi ne ya yi umarni ayi zumunci to ya zama wajibi a daure ayi domin samun wadancan abubuwa dana lissafo a baya. Zumunci tabbas sai an yi hakuri da gaske an kawar da komai aji aki ji, a gani aki gani, ya zama wajibi ayi hakuri a kara da hakuri domin samun dacewa duniya da lahira.
Sunana Hadiza Ibrahim D. Auta, Kaura-Namoda Jihar Zamfara:
Zumunci shi ne kulawa, ta bangaren ziyarar juna ko kuma yanzu da zamani ya zo da waya a dinga jin motsin juna. Saboda abu ne mai muhimmanci a cikin rayuwarmu ta yau da kullum. Domin yana kara dankon kauna tsakanin ‘yan’uwa har ma da abokan arziki na kusa da nesa gabadaya. Yana saka hadin kai shakuwa da fahimtar juna, sannan taimakekeniyar juna idan bukatar hakan ta taso. Abin da ke janyo tabarbarewarsa kuma nuna wariyar launin fata tsakanin mai shi da rashin shi. Sannan rashin kulawar juna tana taka muhimmiyar rawar dakile kofofin sada zumunci. Illar rashin zumunci yana janyo rarrabuwar kai tsakanin dangi da abokan mu’amala kowace iri. Babbar shawarata ga kowa a ajiye kabilanci a zauna da kowa lafiya, ‘yan’uwa da haduwar hanya duka. A dinga tuna juna ana binciken halin da juna suke ciki. A daina yin shakulaton bangaro da lamurran abokan zama ko da haduwar wuccin gadi ballantana wacce jini ya gama ratsawa.
Sunana Sadik Abubakar, ‘Yammata Rijiyar Lemo, Kano:
Zumunci na nufin kyautatawa da jinkai da tausayawa tsakanin ‘yan uwa ta hanyar ziyartar su da nufin saka farinciki a zukatansu da kawar da kowacce irin damuwa da sharri daga gare su, daidai iyawar mutum. Amsa kiran dangi da gayyatar su da taimaka musu da dukiya da kalamai masu taushi da kawar da kai daga kura-kuransu da yi musu addu’ar alheri, duk wannan zumunci ne. Har ma da zuwa duba marasa lafiya da jajanta musu a kan wata asara, da taya su farin cikin samun wani alheri da rufa musu asiri da rike amanarsu da kare mutunci da martabarsu a gabansu ko a bayansu. Wadanda ya kamata a yi wa zumunci su ne dukkan ‘yan’uwa dangi na kusa da na nesa, da makwabta da gajiyayyu. Dangi na nesa za a rika sada zumunci ta hanyar kiran waya da sauran kafafen sadarwa na zamani, idan kuma abu na da muhimmanci sai a taka a je har inda suke. Abin da ke janyo yankewar zumunci akwai son zuciya da rashin sanin muhimmancin sada zumuncin. Wasu mutanen kan dauka sai suna da abin mikawa sannan za su je wajen dan’uwa, wannan kuskure ne. Ka je ku ga juna ku gaisa shi ma zumunci ne. Mai yanke zumunci tun daga duniya ‘yan’uwansa ba za su samu shakuwa da shi ba, za ma a iya mantawa da shi gabadaya. Sannan akwai wani hadisin Manzon Allah (SAW) da ya ce: “Babu wani zunubi wanda ya cancanta Allah ya gaggauta yi wa mai shi ukuba tun daga nan duniya bayan wanda ya tanada a lahira kamar mai yanke zumunci.” Shawara na farko mu ji tsoron ukubar da Allah ya tanadar wa masu yanke zumunci, sannan mu sani shi sada zumunci ba ya nufin dole sai ka ba wa mutum wani abu, kiran waya kawai a gaisa sada zumunci ne. Ya Allah ka ba mu ikon sada zumunci domin saduwa da dukkanin alkhairan da ke cikinsa na duniya da lahira.
Sunana Zainab Abdullahi (Lailat), Jihar Katsina:
Ma’anar sada zumunci dai shi ne kyautatawa da jin kai, tare da ziyartar juna da kuma amsa gayyatar juna idan bukatar hakan ya taso, taya juna murna idan abun murna ya samu da kuma taya juna jaje idan wani ibtila’i ya auku. Har ila yau ma’anar sada zumunci na cikin yi wa juna sallama da kuma yi wa juna sannu idan an yi atishawa, yi wa dan’uwanka addu’a alhalin bai sani ba shi ma wani nau’i ne na zumunci an karbo Hadisi daga Abu Ayyubal Ansari (RA) ya ce “Wani bakauye ya zo wajen Annabi (SAW) ya ce “Fada min abin da zai kusantar da ni ga aljanna, ya kuma nesanta ni da wuta” Sai Manzon Allah ya ce “Ka bautawa Allah shi kadai kada ka hada shi da kowa, ka tsaida sallah, kuma ka bayar da zakka, sannan kuma ka sada zumunci” Wannan hadisin ya nuna mana muhimmancin da zumunci yake da shi, amma abin takaici yanzu zumunci ya zama yasashshe a cikin musulmi, gabadaya an yi watsi da koyarwa Manzon Allah, mai kudi baya zumunci sai da ‘yan uwansa masu kudi, an mayar da zumunci ya zama kwarya ta bi kwarya saboda son zuciya. Manzon Allah (SAW) ya tsoratar da mu akan sakin zumunci tare da yi mana kashedi mai tsanani akan watsar da shi, inda yake cewa a cikin wani hadisi “Idan al’umma ta watsar da zumunci, to wannan al’umma ta dauki hanyar tarwatsewa” Lalle Manzon Allah (SAW) ya yi gaskiya, domin halin da al’umma ta samu kanta a wannan.
Sunana Aminu Adamu Malam Maduri A Jahar Jigawa:
Hakika zumunci abu ne mai matukar muhimmanci, duba da yadda addininmu na musulunci yayi kira akan sada shi, domin samun kyakkyawar mu’amula da shakuwa da kauna a tsakanin ‘yan uwa da abokan arziki, wanda hakan yake dorewa daga iyaye, ‘ya ‘ya, jikoki har da tattaba kunne, kuma hakan yana taimakawa wajen taimakon juna har da aurataiya a tsakani. To shi zumunci ana yinsa da dukkanin Al’umma koda kuwa ba addininku daya ba, amma wanda suka fi muhimmanci sune; kamar ‘yan uwa na jini na kusa dana nesa, makofta da kuma abokan arziki, wadanan su suka fi muhimmanci wajen sada zumunci a tsakani, wanda hakan yake kawo taimakon juna, kaunar juna har da auratayya a tsakani. To magana ta gaskiya tabarbarewar tarbiyya addinin musulunci, kwaikwayon al’adun turawan yamma dama son abun duniya suna daga cikin abubuwan da suka jawo tabarbarewar zumunci a tsakanin Al’umma a wannan zamani, domin yanzu mafi yawan Al’umma basa kokarin sada zumunci sai tabbatar za su samu wani abu. Tabbas na san illar yankewar zumunci, domin yana kawo rabuwar kan ‘yan uwa, rashin taimakon juna, wanda kuma hakan zai jawo rashin ci gaba a tsakanin Al’umma. To shawarata ita ce; ya kamata mu komawa koyarwar addininmu na musulunci dama al’adun mu na Hausa, domin sune suke koyar da hanyoyin sada zumunci dama nuna amanar sosai yadda Al’umma za su yi riko da su wajen sada zumunci, daga karshe nake addu’ar Allah ya bamu ikon sada zumunci da ‘yan uwan mu, abokan arziki dama makofta.