A kan ce, “waiwaye adon tafiya”. Idan an waiwayi abubuwan da suka faru a duniya cikin shekarar 2023, za a ga cewa ana ta fama da yake-yake, da abkuwar rikici a wurare daban daban. Sai dai kuma duk da hakan, akwai huldar kasa da kasa da take ta samun ci gaba a kai a kai, misalin irin wannan hulda ita ce tsakanin kasashen Afrika da kasar ta Sin.
To ko mene ne dalilin da ya sa wannan hulda ke ta samun kyautatuwa? Dalilin shi ne hadin gwiwar da ake yi tsakanin Afrika da Sin na dora muhimmanci ne kan haifar da ci gaba, da raya al’umma.
- Firaministan Kasar Sin Ya Ziyarci Yankunan Da Suka Yi Fama Da Bala’in Girgizar Kasa
- Dalilan Da Suka Jawo Hankalin ‘Yan Kasuwan Ketare Zuwa Sin Kafa Kamfanoni
Misali, a watan Afrilun bana, an kaddamar da tashar jiragen ruwa ta Lekki a tarayyar Najeriya, wadda wani kamfanin kasar Sin gina. Ana sa ran ganin tashar da ta fi girma a yammacin Afrika, za ta samar wa Najeriya kudin shiga da ya kai kimanin dalar Amurka biliyan 360, da guraben aikin yi dubu 170.
Nan gaba kuma, za a hada tashar Lekki da layin dogo, ciki har da layin dogo na “Blue Line” da aka fara yin amfani da bangarensa na farko a watan Satumban bana, wanda shi ma wani kamfanin Sin ne ya gina. Wannan layin dogo ya rage lokacin zirga-zirga na fasinjoji daga fiye da awa 2 zuwa minti 15. Kana bayan da aka kammala bangaren layi na 2, baki dayansa zai iya jigilar kimanin fasinjoji dubu 500 duk rana.
Za mu iya ci gaba da waiwayen wasu batutuwa masu alaka da hadin gwiwar Afrika da Sin da suka faru a shekarar 2023 da muke ciki, wadanda dukkansu suka nuna yadda ake kokarin samar da hakikanin ci gaba.
A watan Yunin bana, an gudanar da bikin baje kolin tattalin arziki da ciniki na Sin da Afrika karo na 3 a birnin Changsha na lardin Hunan na kasar Sin. A wajen bikin, an tattauna batun fitar da karin kayan marmari da na lambu daga nahiyar Afrika zuwa kasar Sin, don tallafawa kokarin kasashen Afrika na zamanintar da aikin gona, da biyan bukatarsu na neman karin kudin shiga. Ban da haka, za a taimaki kamfanonin kasashen Afrika wajen sayar da kayayyaki na wasu tambura 106 a kasuwannin kasar Sin. Ban da haka, an tabbatar da niyyar inganta hadin kan kasashen Afrika da Sin ta fuskar sarrafa amfanin gona, da na’urorin hada kayayyaki. Inda a baki daya aka tabbatar da ayyukan hadin gwiwa kimanin 120 a wajen bikin baje kolin, wadanda darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 10.3.
Sa’an nan, a watan Agustan bana, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ziyarci kasar Afrika ta Kudu, da halartar taron koli na kasashen BRICS, inda ya jagoranci taron tattaunawar shugabannin kasashen Sin da Afrika, tare da takwaransa na kasar Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa. A wajen taron, shugaba Xi ya kaddamar da wasu ayyuka guda 3, na taimakawa kokarin raya aikin gona, da masana’antu, da horar da matasa a nahiyar Afrika, don daidaita wasu matsalolin da kasashen Afrika ke fuskantar, irinsu koma baya a fannin aikin gona, da rashin sana’o’in da ake iya amfani da su wajen raya tattalin arziki, da karancin damammaki na samun ilimi da guraben aikin yi ga matasa, da dai sauransu. Haka zalika, Sin ta yi alkawarin daidaita tsarin cinikin da ake yi tsakaninta da kasashen Afrika, da kara azama ga cinikayyar da ake yi tsakanin kasashen Afrika, da kuma dunkulewar tattalin arzikinsu.
Ban da haka, a watan Oktoban bana, an gudanar da taron dandalin hadin gwiwar kasa da kasa a karkashin laimar shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” karo na 3, inda aka tabbatar da kaddamar da ayyukan hadin gwiwa 369. Har ila yau kuma, taron ya gabatar da takardar bayani don bayyana nasarorin da aka samu wajen aiwatar da shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” da kasar Sin ta gabatar, cikin shekaru 10 da suka gabata. An ce, a nahiyar Afirka kadai, shawarar ta kai ga gina wata babbar cibiyar kandagarkin cututtuka ta Afirka ta zamani a Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha, inda hedkwatar kungiyar kasashen Afirka ta AU take, da sanya kasar Congo Brazaville samun wani babban bankin kasuwanci na kanta, da sanya kasar Zambia samun jarin da yawansa ya zarce dalar Amurka biliyan 2.5, da guraben aikin yi fiye da dubu 10, bisa yankin raya tattalin arziki da ciniki da kasar Sin ta gina a kasar, gami da baiwa mutanen kauyuka 9512 na kasashe 21 dake nahiyar Afirka damar kallon telabijin a gidajensu…A nasa bangare, mataimakin shugaban kasar Najeriya Kashim Shettima, wanda ya halarci taron nan mai alaka da shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” a birnin Beijing, ya ce, “ Aiwatar da shawarar na da muhimmiyar ma’ana ga ci gaban nahiyar Afrika, wanda ya taka muhimmiyar rawa a fannin gina kayayyakin more rayuwa a kasashen Afrika, ciki har da Najeriya.”
Sai dai ko me ya sa ake iya mai da hankali kan kokarin tabbatar da ci gaba a kai a kai yayin da ake hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika? Amsa ita ce, kokarin samar da ci gaba wata babbar ka’ida ce ta kasar Sin, ta fuskar hadin kanta da sauran kasashe. Tun shekarar 2021, kasar Sin ta gabatar da shawarar tabbatar da ci gaba a duniya, wadda ta kunshi bayanan da suka hada da nacewa ga dora mafi yawan muhimmanci kan kokarin samar da ci gaba, da kyautata zaman rayuwar jama’a, da taimakawa biyan bukatun kasashe masu tasowa na samun ci gaban tattalin arziki, da dai sauransu. Sa’an nan dimbin nasarorin da aka samu ta hanyar gudanar da hadin kai tsakanin Sin da Afrika su ma sun shaida cewa, bayan da kasar Sin ta gabatar da shawarar samar da ci gaba a duniya, tana kuma kokarin aiwatar da ita. (Bello Wang)