• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kasashen Duniya Na Kara Zuba Jari A Kasar Sin

byCGTN Hausa
2 years ago
Duniya

Yayin da kasar Sin ta samu bunkasuwar zuba jari daga ketare a wannan shekarar dake daf da karewa, kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya suna ci gaba da yin amfani da tsofaffin dabaru wajen sukar yanayin kasuwanci da tattalin arzikin kasar Sin.  

Idan kana bibiyar sabbin labarai kan tattalin arzikin kasar Sin ko jarin waje a shafukan yanar gizo na kafofin watsa labaru na kasashen yamma, na tabbata za ka gano wasu labarai marasa dadi game da yanayin tattalin arzikin kasar ko kuma jarin waje.

  • An Wallafa Littafin Xi Jinping Game Da BRI Bugun Shekarar 2023
  • An Fara Gina Cibiyar UHD Highland Ta CMG

Maganar gaskiya ita ce yawancin wadannan labarun ba daidai ba ne. Kasar Sin ta inganta yanayin kasuwancin kasar akai-akai tun farkon shekarar 2023 lokacin da ta bullo da matakai da dama don daidaita zuba jarin waje, wanda ya jawo karin kamfanonin waje zuba jari a kasar Sin, wanda kuma ke nuni da yadda tattalin arzikin Sin ke kara bunkasuwa cikin sauri.

Wani bincike da Faransa ta gudanar ya nuna cewa, yadda kasar Sin ta kara yawan jarinta na waje kai tsaye wato FDI, ya kara wa masu zuba jari kwarin gwiwa game da halin da tattalin arzikin kasar ke ciki, lamarin da ya sa wasu manazarta ke hasashen cewa, kamfanonin kasa da kasa sun yanke shawarar “karfafa kasuwancinsu a kasar Sin”, a cewar wani binciken da hukumar hidimar kudi wato “BNP Paribas Asset Management” ta Faransa ta yi.

Kasar Sin ta zama cibiyar zuba jarin kasashen waje saboda yanayin tattalin arzikinta dake maraba da kamfanonin kasashen waje. Ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta bayyana cewa, a cikin watanni 10 na farkon shekarar 2023, an kafa sabbin kamfanoni 41,947 da suka zuba jari a kasashen waje, lamarin da ya nuna babban ci gaban da aka samu da kashi 32 cikin 100 na jarin waje kai tsaye (FDI). FDI cikin kasar Sin ya karu da kashi 110.3, kashi 94.6, kashi 90, kashi 66.1, da kashi 33 cikin dari daga kasashen Canada, Birtaniya, Faransa, Switzerland, da Netherlands bi da bi. Wannan karuwar na da nasaba da yadda kamfanoni na kasa da kasa suke son zuba jari a kasar Sin.

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Bugu da kari, jarin waje da fannin masana’antu ya samu ya kai Yuan biliyan 283.44 na kasar Sin, wanda ya nuna karuwar kashi 1.9 cikin dari idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. Na’am, wannan labari ne mai ban sha’awa, la’akari da munanan bayanai da wasu kafafen yada labarai na kasa da kasa ke yadawa game da daidaituwar tattalin arzikin kasar Sin. Bayanan nasu ba su da tasiri yayin da saka hannun jari na yau da kullun na kamfanonin ketare ke karuwa. (Muhammed Yahaya)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci
Daga Birnin Sin

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?
Daga Birnin Sin

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
Next Post
APC

Zaben Cike Gurbi: APC Za Ta Sayar Da Takardar Tsayawa Takarar Sanata Naira Miliyan 20

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Tinubu

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk 

October 7, 2025
Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version