Gwamnatin jihar Zamfara ta dauki matakin rufe kasuwannin sayar da shanu 11 a sassa daban-daban na jihar har sai baba-ta-gani.
Kwamishinan yada labarai na jihar, Munnir Haidara ne ya fitar da sanarwar a ranar Laraba, inda ya ce, an yanke shawarar rufe wadannan kasuwannin ne sakamakon rahotannin tsaro da ke nuni da cewa, ‘yan fashin daji na amfani da wadannan kasuwanni wajen sayar da shanunsu da suka sato.
- An Masa Daurin Rai Da Rai Saboda Yin Fyade A Masallaci A Bauchi
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Sama Da 100 a Kauyen Filato
Kasuwannin da umurnin ya shafa sun hada da Tsafe da Bilbis a karamar hukumar Tsafe, da kasuwar Jangebe a karamar hukumar Talata-Mafara, da kasuwar Wuya a karamar hukumar Anka.
Bugu da kari, kasuwar Magamin Diddi da ke karamar hukumar Maradun, da kasuwar Galadi a karamar hukumar Shinkafi, da kasuwar Mada a karamar hukumar Gusau, da Sabon Birnin Dan-Aii a karamar hukumar Birnin Magaji duk umurnin ya hada da su.
Haka kuma, an hada da kasuwannin Kokiya, Chigama, da Nasarawar Godel, da ke cikin karamar hukumar Birnin Magaji.
Gwamnati ta umurci hukumomin tsaro da su tabbatar da bin umarnin doka.
Haidar ya bukaci al’ummar jihar da su bi wannan umarni tare da hada kai da gwamnati a kokarinta na kawar da ayyukan ‘yan ta’adda.