Shekarar 2023 shekara ce ta cika shekaru 10 da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar “Ziri daya da hanya daya”. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta gabatar da nasarorin da aka cimma kan raya shawara din mai inganci a wannan shekara a wani taron manema labarai da aka saba yi a yau Laraba ranar 27 ga wata.
Jami’ar ta bayyana cewa, a bana, an samu ci gaba akai-akai kan ayyukan hadin gwiwa ta fannonin tattalin arziki da cinikayya da zuba jari game da shawarar “Ziri daya da hanya daya”. Alal misali, an kaddamar da tashar ruwa mai zurfi ta Lekki dake kudancin Najeriya da sauran wasu ayyuka, wadanda ke karfafa mu’amala da sadarwa tsakanin kasashe da yankunan da abin ya shafa. An kuma kammala aikin hedikwatar cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Afirka da kasar Sin ta ba da taimako wajen ginawa a farkon shekarar nan. Baya ga haka, wasu kananan ayyuka masu kyau da suka shafi zaman rayuwar al’umma, irin su shirin ba da horo na Luban, aikin “Bright journey”, fasahar Juncao, shinkafar aure, da kuma kwayar maganin artemisinin da dai sauransu, na ci gaba da amfanar da kasashe masu tasowa da kuma samar da sakamako mai kyau.
Jami’ar ta kuma jaddada cewa, kasarta na fatan daukar bikin cika shekaru 10 da gabatar da shawarar “Ziri daya da hanya daya” a matsayin wani sabon mafari, don yin hadin gwiwa tare da bangarori daban-daban, wajen sa kaimi ga samun bunkasuwar shawarar mai inganci, da kuma kara sa kaimi sosai kan gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga bil’adama. (Mai fassara: Bilkisu Xin)