Babban mai ba da shawara kan tsaro (NSA) ga shugaba Bola Ahmad Tunibu, Malam Nuhu Ribadu, ya yaba wa sarakunan gargajiya bisa kokarin samar da zaman lafiya da hada kan jama’a a Jihar Adamawa.
Malam Nuhu Ribadu, ya bayyana haka lokacin da ya ziyarci fadar manyan sarakunan yankin Bachama, Lunguda da Batta, domin ta ya sarakunan murnan bikin Kirsimeti.
- Wasu Rahotanninmu Na Musamman A 2023: Asalin Garkin Abuja Da Ya Shafe Sama Da Shekara 177 Da Kafuwa
- Yadda Muka Yi Da ‘Yan Bindigar Da Suka Sace Iyalina – Sarkin Kagarko
Babban mai bada shawara kan tsaron da ya samu wakilcin shugaban jam’iyyar APC na Jihar, Barista Idris Shu’aibu, ya roki sarakunan da su ci gaba da bada gudunmawa domin tabbatar da samun zaman lafiya da hadin kai mai dorewa a jihar da kasa baki daya.
Ya ci gaba da cewa “Ribadu ya bukacie mu kawo muku gaisuwa, saboda yanayin aikin ofis da bai bashi damar zuwa da kansa ba,
“Ya bukaci mu wakilce shi, mu kasance da ku a bukin Kirsimeti, kuma yana yi muku barka da shiga sabuwar shekara 2024.
“Haka kuma ya bukaci da mu gode muku, bisa rawar da kuke takawa wajen samun zaman lafiya, hadin kai da fahimtar juna tsakanin jama’armu, ya alkawarin hada hannu da sarakunan domin cimma zaman lafiya da ci gaba a kasa” bukaci da hakan ya ci gaba” in ji Ribadu.
Da suke maida kalami a lokuta daban-daban, sarakunan gargajiyar ma su daraja ta daya a jihar, Sarkin Numan Hama Bachama, Dr. Daniel Shagah Ismail, Kpawo Nomwe, Gilongo Diya, da sarkin Demsa, Hama Bata, Homun Alhamdu Gladson Teneke da kuma Kwandi Nunguraya, Kuruhaye Dishon Dansanda II, sun gode wa Malam Nuhu Ribadu.
Sun kuma yi alkawarin ci gaba da bada goyon baya ga tsare-tsare da manufofin gwamnatin tarayya, domin cimma nasara mai dorewa kan zaman lafiya a yankin da suke shugabanta, domin ci gaban Nijeriya.