ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wasu Rahotanninmu Na Musamman A 2023: Asalin Garkin Abuja Da Ya Shafe Sama Da Shekara 177 Da Kafuwa

Mun wallafa a 20 ga Janairu, 2023

by Leadership Hausa
3 years ago
Garki

Da yake masu karin magana sun ce ‘waiwaye adon tafiya’. LEADERSHIP Hausa ta zakulo wasu daga cikin rahotanni na musamman da ta wallafa a 2023 domin sabunta ilmantarwa da fadakarwar da ke ciki domin kara daukar darasi musamman daga wadanda abin ya shafa da kuma sauran al’umma. Ga su nan daya bayan daya kamar haka:

Garki Abuja wani gari ne mai dadadden tarihi wanda mafi akasarin mutanen da suke cikinsa Hausawa ne da suka fito daga garuruwan Hausawa daban-daban na Arewa. Mutum da ya shiga shi cikin Garki ya san cewa lalle ya zo inda Hausawa suke kamar yadda masu karin magana ke cewa “da gani babu tambaya”. Duk irin sarautun da ake da su a kasashen Hausa can ma akwai su kamar irin su Sarkin Aska, Sarkin Fada, Sarkin Fawa, Sarkin Samari, da dai sauran sarautun gargajiya wadanda aka sani. Wani babban ala’amari game garin Garki shi ne yadda ake gudanar da harkokin kasuwanci, sai mutum ya yi tsammanin kamar ma duk garin kowa dan kasuwa ne. Musamman ma idan mutum ya bi ta wani layin sai zaci kamar yana cikin Kasuwar kantin Kwari na Kano ne.

  • Sin Ta yi Nasarar Harba Tare Da Gwada Taurarin Dan Adam Na C Karo Na 24
  • NAF Ta Lalata Haramtattun Wuraren Tace Mai Guda 6 A Ribas 

Bugu da kari, suna da masu dadaddun sana’o’in da aka sans u a garuruwan Hausawa tun fil-azal kamar Dukanci, Kira, Wanzanci da sauransu wanda wani na iya mamakin cewa akwai irin wadannan sana’o’in kuma a tsakiyar Babban Birnin Tarayya Abuja. Babban Sarkin Yanka da Garki ke karkashin masarautarsa shi ne SA’PEYI, ALHAJI DAKTA USMAN NGA KUFI. Wakilinmu IDRIS ALIYU DAUDAWA, ya yi takakkiya zuwa Garki inda ya tattauna da Hakimin Garki wanda har ila yau shi ne Sarkin Hausawan Masarautar Garki, UMARU ABUBAKAR ABDULLAHI wanda ya yi magana ta bakin Sarkin Samarin Garki, ABDULWAHAB MUSA a fadarsa da ke kwaryar Garki kan tarihin kafuwar garin.

ADVERTISEMENT

Ga kadan daga tambayoyin da ya amsa:

Tarihin Hausawan Garki…

LABARAI MASU NASABA

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

Akwai wasu maganganun kan tarihin da mutane ke samu ya kuma zama sabani da shi. Asalin tarihin Hausawan Garki matafiya ne wadanda za a iya kiran sunansu da Fatake mutanen da ke kasuwanci tsakanin Arewacin Nijeriya da kuma Kudancinta.

Suna tafiya idan suka zo nan wurin da yanzu ake kira da suna Garki suna yada zango wannan tarihi da nake ba ka ya fara ne daga shekarar 1845, tun suna yada zango za ka ga su mutane ne wadanda suke kawo kayayyaki daban-daban suna kuma sayarwa.

Toh, suna sayar da kayayyakin da suka kawo, in sun sayar, in lokacin tafiyarsu ya yi zuwa gida sai su shirya su koma gida, da haka ne har sai aka kawo wani lokaci wanda suka ga yafi dacewa su zauna.

Asalin mutumin da ya fara zama na dindindin a wannan gari da ake kira Garki shi ne Malam Muhammadu na Makarfi, wanda shi ne ya zama Sarki na farko a wannan yanki ko Gari namu wanda mu muka fi kiransa da Garkin Hausa. Ya fara mulkinsa a shekara 1865 Allah ya yi masa rasuwa a shekara ta 1910 ya yi shekara 45 yana mulki.

Daga nan kuma sai Malam Ahmadu wanda ya fara sarautar shi a shekarar 1910, ya rasu a 1925, ya yi shekara 15 yana mulkin, daga nan sai Abdullahi wanda ya fara daga shekarar 1925 zuwa 1938 ya yi shekara13, sai Abdullahi Maje Ruboci daga1938 zuwa 1968 wanda ya yi shekara 30 a kan mulki.

Abubakar Abdullahi shi ne Sarkin Hausawa na biyar har ila yau kuma mahaifin Sarkin Hausa na yanzu ya yi sarauta ne daga 1968 zuwa 2007 ya yi shekara 49. Daga nan nan a jerin Sarakunan Husawan Garki sai Umaru Abubakar Abdullahi shi ne Sarkin Hausawa na yanzu da aka nada shi a shekara ta 2007 Sarki na shida.

Abin da ya faru shi ne mahaifinsa da yaga baya da lafiya sai ya kira shi a matsayinsa na babban dansa, ya kira jama’arsa ya sheda masu ya nada shi a matsayin shi ne Sarkin Hausawa.

Saboda ba ya iya tafiyar da mulki na jagorancin al’ummar Hausawa a matsayin shi na Sarkinsu sanadiyar rashin lafiyar da yake fama da ita, a wancan lokacin da ma shi mahaifin nasa tsohon wanda yake karbar ma gwamnati haraji ne, har daga baya ta zo ta nada shi Dagaci. Lokacin da aka nada shi Dagaci ne sai rashin lafiyar ya yi mashi tsanani, yanzu ma likkafa ta yi gaba saboda an nada shi a matsayin Hakimi na Garki Hausa.

Domin sake cikakkiyar hirar, a nemi jaridarmu ta ranar 20 ga Janairun 2023.

Garki
Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?
  • Leadership Hausa
    An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu
  • Leadership Hausa
    Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja
  • Leadership Hausa
    Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

MASU ALAKA

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu
Rahotonni

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Umarnin Kawo Karshen Matsalar Tsaro
Rahotonni

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

September 5, 2026
Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed
Rahotonni

Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

September 5, 2026
Next Post
Akidar Siyasar Malam Aminu Kano Da Ta ‘Yan Siyasar Yanzu A Mizani –Farfesa Habu

Akidar Siyasar Malam Aminu Kano Da Ta ‘Yan Siyasar Yanzu A Mizani –Farfesa Habu

LABARAI MASU NASABA

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

September 10, 2026
Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

September 10, 2026
Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026
Garki

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
Garki

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.