Biyo bayan amincewar majalisar dokokin Jihar Adamawa, kan kiyasin naira miliyan dubu biyu da dari biyu da ashirin da biyar da miliyan takwas da yan kai (N225.893b), a matsayin kasafin kudin jihar na shekarar 2024, gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya rattaba hannu.
Da yake jawabi kafin rattaba hannu a gidan gwamnatin jihar, gwamna Ahmadu Fintiri, ya gode wa mambonin majalisar dokokin jihar bisa amincewa da kasafin a lokacin da ya dace.
- Samar Da Tsaro: Ribadu Ya Yaba Wa Sarakunan Gargajiya A Adamawa
- Bankwana Da 2023: Wasu Abubuwan Da Suka Dauki Hankali A Fannin Tsaro
Gwamnan ya bai wa mambonin majalisar tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kula da kyakkyawar alaka da fahimtar da ke tsakanin bangaren zartaswa da bangaren majalisar dokokin jihar.
Ya ce “Za mu tabbatar da yin aiki da yadda wannan kasafin kudin yake bisa gaskiya, kiyaye doka da horo, jama’a za su ci gaba da samun ababen more rayuwa karkashin gwamnatinmu” in ji Fintiri.
Da yake yi wa manema labarai karin bayani kwamishinan ma’aikatar kasafi da tsara tattali na jihar Emmanuel Pridimso, ya ce an yi tanadin ababen more rayuwa ma su gwabe kunshe cikin kasafin kudin, bisa kuduri 8 na gwamnatin jihar.