A halin yanzu bincike ya nuna cewa, yawancin ‘yan Nijeriya masu hulda da bankuna sun koma rungumar bashin banki don rage radadin da ake fuskanta sakamakon tsadar rayuwa a kasar nan.
An samu karuwar bukatar karbar bashi a watan Agusta fiye da yadda yake a cikin shekara 4 da suka wuce, wannan kuma yana faruwa ne saboda matalar tattalin arziki da al’umma suka shiga a ‘yan shekarun nan.
- Yadda Muka Yi Da ‘Yan Bindigar Da Suka Sace Iyalina – Sarkin Kagarko
- Gwamnan Katsina Ya Yi Wa Ma’aikatan Jihar Ƙarin ₦10,000 Kan Albashi, ‘Yan Fansho ₦5,000
Kididdiga na baya-bayan nan daga Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya nuna cewa, bashin da masu hulda da bankuna suka karba ya tashi da kashi 16.9 zuwa naira tiriliyan 2.99 a watan Agusta zuwa yadda yake a halin yanzu na naira Tirilyan 2.56, ya kuma ci gaba karuwa a shekarun da suka biyo baya.
“Idan aka samu hauhawar farashin kaya masarufi a daidai lokacin da tattalin arzikin al’umma kuma yake tabarbarewa dole a samu irin wannan cin bashin da ake gani, al’umma na komawa ga cin bashi ne don warware matsaloilin da suke fuskanta na yau da kullum,” in ji wani masanin tattalin arziki, Temitope Omosuyi.
Ya kuma kara da cewa, al’amurran kasuwanci a kasar nan ya fuskanci gaggaurujin matsala, inda da yawan ‘yan Nijeriya suka rasa ayyukansu wasu harkokin kasuwancin ma suka durkushe baki daya, wanda haka ya kara tabarbarewa harkokin rayuwa.
“Hukumar Kididdiga ta Kasa ta bayyana cewa, abinci shi ne kashi 50 na abin da al’umma ke nema a kullum a raywarsu, sai kuma abin takaicin shi ne abincin ya yi tashin gwauron zabi, abin kuma da yasa ya zama dole al’umma su rungunmi bashi don tsira da mutuncinsu,” in ji shi.