Itaciyar magarya na da dimbin tarihi yadda ya kamata, sannan tana maganin abubuwa masu daman gaske da suka hada da cutukan daji, ciwon miki (idan wani tsiro ko kari ya fitowa mutum a jikinsa).
Idan aka samu ganyen magarya aka busar da shi, sai a daka a tankade shi sosai. Don haka, ga mai ciwon gyambo ko kuma wanda yake da ciwon da ya ki warkewa, har ake tunanin ko shafar sa aka yi ko kuma wani abu daban aka yi masa, kamar sihiri da sauran makamantansa, sai a nemi wannan ganye na magarya a yi amfani da shi.
- Bankwana Da 2023: Wainar Da Aka Toya A Fagen Wasanni
- Samar Da Tsaro: Ribadu Ya Yaba Wa Sarakunan Gargajiya A Adamawa
Da farko dai, za a nemi ruwan dumi a tafasa shi sosai; sai a samu garin ganyen magaryar a zuba a ciki, bayan ya dan huce sai a wanke ciwon da shi. Bayan wanke ciwon, sai kuma a kawo garin magaryar tankadadde a zuba a kan ciwon ko gyambon, wanda ya ki ci ya ki cinyewa; daga nan in sha Allahu za a samu waraka.
Har ila yau, ana yin maganin sihiri da ganyen magarya, ma’ana; ga duk wanda ake tunanin an yi masa sihiri, sai a nemo ganyen magarya guda bakwai a mutsittshika su, domin kuwa sihiri ya kasu kashi bakwai, akwai wanda ake raba mutum da mutum, akwai wanda ake sa wa mutum cuta ya rika yawan kwanciya, akwai wanda ake kashe wa mutum kasuwa, akwai kuma wanda ake sa wa mutum rashin lafiya da sauran makamantansu.
Saboda haka, da zarar an fahimci an yi wa mutum daya daga cikin wadannan sihiri, a samo ganyen magarya guda bakwai a murje su da hannu, a zuba a ruwa.
Daga nan kuma, akwai ayoyin alkur’ani da ake bukatar a tofa a cikin wannan ruwa, wanda ya hada da suratul a’arafi aya ta dari da sha bakwai zuwa aya ta dari da ashirin da biyu, sai suratul Yunus aya ta saba’in da tara zuwa aya ta tamanin da biyu.
Haka nan kuma, suratul Daha aya ta sittin da biyu zuwa ta saba’in. Daga nan, za a tofa Falaki da Nasi da Ayatul kursiyyu a ciki. Kazalika, za a karanta Kulya ayyuhal kafiruna a tofa a cikin ruwan da aka zuba wannan ganyen magarya, sai a ba wa wanda ake tunanin an yi wa wannan sihiri ya sha, ragowar ruwan kuma sai ya shafe jikinsa baki-daya; za a samu waraka da yardar Allah.