A yayin da mabiya addinin Kirista suke bikin Kirsimeti, ‘yan gudun hijira daga Kudancin Kaduna sun koka dangane da yadda ake tsauwala musu kudin gidan haya sakamakon harin ‘yan ta’adda.
‘Yan gudun hijirar da ke samun mafaka a Garin Katari da cikin Garin Kachiya duk a karamar Hukumar Kachia a jihar sun bayyana cewa bikin kirsimetin wannan shekara ta zo musu cikin tashin hankali da fargabar harin ‘yan ta’adda.
- Amfanin Ganyen Magarya Ga Lafiyar Dan’adam
- Za Mu Nome Dazuka Don Magance Matsalar Tsaro A Neja – Bago
A ziyarar da wakilinmu ya kai karamar hukumar Kachia, ya tarar da ‘yan gudun hijarar sama da guda dubu daya da suka fito daga kauyen Bishini da Impi wadanda suka bar gidajensu bisa fargabar harin ‘yan ta’adda sun bazama neman gidajen haya domin samun damar gudanar da bikin kirsimeti.
Hakimin gundumar Bishini, Mista Yohanna Musu, ya ce sun bar gidajensu sun shigo Garin Kachiya da Katari domin neman dakin haya. Ya ce a makon da ya gabata ana kama dakin haya a kan naira dubu daya a duk mako, amma yanzu ya koma naira dubu uku, baya ga matsalar rashin abinci da suke fama da ita sakamakon fargabar harin ‘yan ta’adda da suka addabi garin nasu.