Jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) sun kama wani damin miyagun kwayoyi da aka shirya kai wa ‘yan bindiga a jihohin Zamfara da Kebbi.
Kakakin hukumar NDLEA, Femi Babafemi ya ce, an kama Yusuf Yahaya mai shekaru 45 a jajibirin Kirsimeti a kan hanyar Legas zuwa Ilorin dauke da kwayoyin masu nauyin kilo 31 acikin wata motar bas ta kasuwanci da ta taso daga Ibadan, jihar Oyo zuwa jihar Kebbi.
- An Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Dawo Da Aikin Samar Da Wutar Lantarki Ta Mambila
- ‘Yan Gudun Hijira Sun Koka Da Tsadar Gidan Haya Da Abinci A Kudancin Kaduna
“Bincike na farko ya nuna cewa, miyagun kwayoyin ana kai wa ‘yan bindiga ne a yankin Kebbi da Zamfara,” in ji NDLEA.
Hukumar NDLEA ta kuma kama wasu masu kasuwanci a kasar Qatar, Agu Evidence Amobi, da Uchegbu Onyebuchi Obi tare da wasu haramtattun kwayoyi a filin jirgin sama na Murtala Muhammed (MMIA) da ke Ikeja, Legas.