• English
  • Business News
Saturday, November 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hukumar Zaɓen Kasar Laberiya Ta Karrama Shugaban INEC Da Lambar Yabo

by Sulaiman
2 years ago
Laberiya

Hukumar Zaɓe ta Laberiya (NEC) ta yi jinjina da damƙa kambin yabo ga Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, bisa ƙoƙari da muhimmiyar rawar da ya taka wajen ƙara wa dimokuraɗiyya karsashi a Nijeriya.

Wannan karramawa ta fito ne daga Shugabar Hukumar Zaɓen Laberiya, Madam Davidetta Browne Lansanah, a ranar Juma’a, a Monrovia, babban birnin ƙasar.

  • Da Dumi-dumi: NAHCON Ta Kara Wa’adin Biyan Kujerar Aikin Hajjin 2024
  • Tudun Biri: Gwamna Uba Sani Ya Kaddamar Da Kwamitin Sa Ido Kan Rabon Gudunmawa

An damƙa masa kambun girmamawar ne a wurin taron sanin makamar aiki da aka shirya wa ma’aikatan hukumar zaɓen Laberiya, wanda Farfesa Yakubu ya gajoranci horaswar.

A cikin jawabinta, Lansanah ta nuna farin ciki da gamsuwa da irin basira da kyawawan tsare-tsaren da INEC da Yakubu su ka shimfiɗa wa Hukumar Zaɓen Laberiya, wanda ta ce ya ƙara wa matakan shirya zaɓuɓɓukan ƙasar inganci da nagarta.

Ta nuna godiya ga Farfesa Yakubu, a madadin Hukumar Zaɓen Laberiya, bisa ga gagarumar rawar da ya taka wajen ƙarfafa dimokuraɗiyya da matakan kafa dimokuraɗiyyar a Laberiya.

LABARAI MASU NASABA

Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

Da ta ke tuna rawar da gudunmawar da ya bayar a matsayinsa na Shugaban Ƙungiyar Shugabannin Hukumomin Zaɓe na Ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS), Lansanah ta lissafo yadda ya tafiyar da ƙungiyar bisa nuna kishin aiki da bin ƙa’idoji. Ta kuma jinjina masa dangane da yadda ya riƙa ba ta goyon baya a matsayinta na Shugabar Hukumar Zaɓe ta Laberiya.

Farfesa

Da ya ke nuna godiya bisa karamcin da aka yi masa, Farfesa Yakubu ya bayyana farin ciki dangane da karramawar da Hukumar Zaɓen Laberiya ta yi wa INEC.

Haka kuma ya nuna muhimmancin nagartattun ayyuka da tsare-tsaren da ma’aikatan INEC su ka bijiro wa ma’aikatan hukumar zaɓen Laberiya.

Ya tuno da irin rawar da INEC ta bayar lokacin tsare-tsaren shirya zaɓen shugaban ƙasa a Laberiya da aka yi cikin 2017, sai kuma gudunmawar da INEC ɗin ta bayar a zaɓen raba-gardama cikin 2020, wanda ECOWAS ta gudanar.

Yakubu ya nuna yadda INEC ta taimaka wa hukumar zaɓen Laberiya wajen gina wa ƙasar turbar rajistar masu zaɓe ta hanyar tsarin na’urar tantance masu katin rajista.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza
Labarai

Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

November 8, 2025
Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga
Labarai

Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

November 8, 2025
Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya
Manyan Labarai

Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya

November 8, 2025
Next Post
Jawabin Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar Sin Game Da Cika Shekaru 45 Da Kulla Huldar Diflomasiyya Tsakanin Sin Da Amurka

Jawabin Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar Sin Game Da Cika Shekaru 45 Da Kulla Huldar Diflomasiyya Tsakanin Sin Da Amurka

LABARAI MASU NASABA

Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

November 8, 2025
Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

November 8, 2025
Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

November 8, 2025
Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

November 8, 2025
Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

November 8, 2025
CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

November 8, 2025
CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

November 8, 2025
Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong

Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong

November 8, 2025
Ta’aziyyar Rasuwar Jarumin Kannywood, Malam Nata’ala

Ta’aziyyar Rasuwar Jarumin Kannywood, Malam Nata’ala

November 8, 2025
Kamfanoni Masu Jarin Waje Na Samun Kwarin Gwiwa Daga CIIE

Kamfanoni Masu Jarin Waje Na Samun Kwarin Gwiwa Daga CIIE

November 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.