MUKHTAR SHUAIBU, mahaifin daya daga cikin yara bakwai da aka samu a Jihar Kano da ake zargin wasu sun sace daga Jihar Bauchi tare da kokarin sayar da su har da canza musu suna, ya bayyana irin tashin hankalin da suka shiga lokacin da ‘ya’yansu suka bace a tattaunawarsa da wakilinmu, KHALID IDRIS DOYA kamar haka:
Ka gabatar mana da kanka…
Sunana Muktar Shuaibu daga unguwar Federal Low Cost a cikin garin Bauchi.
Ta yaya satar yaran nan ta shafeka?
Kwarai da gaske lamarin ta shafeni. Daga cikin yaran, akwai wacce ake ce mata Asiya Mukhtar ‘yar shekara biyar ni ne mahaifinta. An sace ta ne ranar 8 ga watan Disambar 2023 da misalin karfe 10 na safiya.
Ya aka yi aka sace ta?
Hakan ya faru ne sakamakon an aike ta shago a kofar gidanmu a kan ta leka shagon ko an bude ko ba a bude ba ta zo ta fada wa mahaifiyarta. Fitar da ta yi ke da wuya, abun da bai wuce a yi cikin minti daya zuwa biyu ba, uwar ta ga ta wuce har minti biyar, sai ta fita ta leka ba ta gan ta ba. Nan take ta dawo ta dauki hijabi ta ce min ita fa ta aiki Ihsan amma ba ta ganta ba, bar ta je shagon ta duba. Ta je shagon ta duba aka ce mata yarinya dai ba ta zo shagon ba gaba daya.
Nan da nan bayan kamar mintina 30, sai na kai rahoto a ofis ‘yansanda da ke kusa da mu. Bayan nan, na je wajen masu unguwannin Federal Lowcost dukka na sanar musu halin da ake ciki tare da zuwa ofishin ‘yansanda na Dutsen Tanshi nan ma na kai rahoto aka dauki bayanaina. Suka ce min idan har zuwa yamma yarinya ba ta dawo ba na je na kai rahoto zuwa shalkwatan ‘yansanda, ban jira ma yammar ta yi ba na ja kai rahoton can.
Haka kuma na je gidajen rediyo dukka babu labari, duk inda ya dace dai mun kai rahoton bacewar ‘yarmu. Shiru kake ji, mu kuma hankalinmu na kara tashi.
Shiru-shiru dai sai muka samu labarin cewa an samu wani yaro a Kano kuma dan Bauchi ne, cewa an sace shi kuma an kama wacce ta sace shi a tashar mota a Mariri a lokacin da wata mata take kokarin tafiya da shi zuwa Legas. Kuma aka ce an samu labarin akwai wata mata da take sayar musu da yara daga Bauchi. Nan fa na tashi na kama bibiyar lamarin har na samu wanda ya kawo cikiyar yaron.
Da aka zo sai aka kama wacce take sayar mata da yaro daga Bauchi, muka ce tun da matar nan tana yankinmu ne domin Federal lowcost da Zango babu nisa duk yadda aka yi ta san wanda ya saci yarinyata, ko kuma inda yarinya take don haka muma za mu yi ta bibiya don mu samu karin haske.
Ita wannan matar da kuke zargi da cinikin yaran a Bauchi kun santa kuma mene ne sunanta?
Sunanta Ruth Yarima kuma yayanta ma gidansa na layinmu. Don haka mun santa, sannan mutanen unguwarmu da dama sun santa.
Bayan da aka kamata ita Ruth daga Bauchi sai me ya faru?
Nan dai muka ji labarin cewa an samu wasu yara ‘yan Bauchi dukkansu da aka sace, amma za a ci gaba da bincike, in an ji labarin akwai yaranmu za a sanar da mu.
Cikin ikon Allah da aka je aka samu yaran, ‘yata ce ma a duk cikin sauran yaran ta iya bayanin sunanta na asali, ban da sunan da wadanda suka sace su suka sanya mata.
Kamar ya sunan da suka sanya mata?
Idan sun sace yara sai su canza musu suna da kuma addini tare da horar da su kafin su dauka su sayar a garuruwan Kudu. To ni ita yarinyata ba ta jima ba, domin ba ta wuce sati biyu ba a hannunsu, ba ta mance da wasu abubuwan ba. Ta iya fadin sunanta da muka sanya mata da sunana kuma ta ce ita ‘yar Bauchi ce. Aka tambaye ta a ina kike a Bauchi, sai da ta yi bayani har masallacin da ke kusa da kofar gidanmu ta kuma fadi sunan makarantar da take.
Daga cikin ‘yansandan da suka kamata na Kano ya ce ya yi aiki a Bauchi, akwai wanda ya sani a unguwarmu, bari ya tura masa hoton yarinyar a yi cigiya. Yana turo masa, sai mutumin ya bai wa limamin masallacin Juma’a na Federal Lowcost domin a yi cigiya, nan take a cikin masallacin wasu suka ce sun san ‘yata ce. Nan dai aka zo har masallacin kofar gidanmu aka neme ni tare da ba ni lambar wanda aka turo masa da hoton muka yi magana da shi.
An ce mu je Kano tare da hotuna guda biyu wanda aka dauka tare da yarinya da kuma shaidar takardar haihuwarta da mahaifiyarta domin a tabbatar da cewa ‘yarmu ce. Kafin ma mu tafi, sai aka sake turo hotonan wasu yaran Bauchi ana neman iyayensu.
An tura hotonan a ofishin ‘yansanda da ke Dutsen Tanshi, domin dukka iyayen da yaransu suka bata sun je sun kai rahoton hakan a wajen. Nan take DCO ‘yansanda da ke can ya kira iyayen da suka kawo rahoton domin su zo ko za su gane yaransu, Allah ya taima dukkanin yaran da aka turo an gane iyayensu.
Nan dai muka shirya muka tafi gaba dayanmu Kano a ranar Juma’a 22 ga watan Disamba, inda muka je shalkwatar ‘yansanda da ke Kano aka dauki bayananmu kuma aka tabbatar da cewa wadannan yaran ‘ya’yanmu ne.
Zuwa yanzu yaran suna hannunku?
Eh, Gwamnatin Bauchi ta mika mana ‘ya’yanmu bayan ta amso su daga hannun gwamnatin Kano.
Wani tashin hankali ka shiga lokacin da yarinka ta bace, kuma da aka same ta ya kuka ji?
Gaskiya mun yi matukar farin ciki lokacin da muka tabbatar an samu yarinyarmu, farin cikin ma ya wuce a misalta. A lokacin da aka sace yarinyar nan hankalina a tashe yake. Wallahi ni da mahaifiyarta ko barcin awa daya ba mu iya yi. Mun ga tashin hankali matuka, ko abinci ba ma iya ci yadda ya kamata.
Wani kira kuke da shi ga gwamnati?
Muna kira ga gwamnati da ta sanya ido, sannan muma iyaye mu kara kula. Sannan babban kiran da nake da shi ga gwamnati da hukumomin tsaro da sauran kungiyoyin da abun ya shafa da su tabbatar da sun yi tsayuwar daka har a hukunta wadanda aka samu da laifin satar yaranmu da sayar da su. A tabbatar an bincike su sosai domin gano kila ko suna da kungiya ko masu tallafa musu ko kuma wakilansu da har zuwa yanzu ba a kamasu ba, domin a tabbatar an zagolo sauran wadanda ba a kama ba zuwa yanzu.
…Gwamnan Kano Ya Jagoranci Sake Hada Yaran Da Aka Sato Daga Bauchi Da Iyayensu
Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir ya jagoranta sake hada yaran da aka sato daga Jihar Bauchi su 7 da iyayensu.
Hakan na kunashe cikin jawabin da daraktan yada labaran gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya raba wa manema labarai a Kano.
Gwamnan ya jinjina wa kokarin rundunar ‘yansandan Jihar Kano karkashin jagorancin kwamishina, Muhammad Hussain Gumel. Ya bayyana matukar damuwarsa bisa yadda aka sato yaran tun daga Bauchi tare da yunkurin sayar da su a jihohin Anambara da Legas.
Kazalika, gwamnan ya bukaci iyayen yaran da su kara himma wajen kula da ‘ya’yansu, sannan ya yi kira ga takwarorinsa gwamnoni musamman gwamnan Bauchi da ya dauki matakin gaggawa domin damke wadanda ake zargin da aikia wannan mummunan lamari.
Rundunar ‘yansandar Jihar Kano ta samu nmasarar damke mutum 9 da ake zargi da aikata laifin a tashar motar Dake Mariri a lokacin da suke kokarin tserewa da yaran zuwa Jihar Legas.