A halin yanzu Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya (NPA) ta hada hannun da Karamar Hukumar Apapa wajen samar wa al’ummar da ke zaune a yankin Apapa tsaftaccen ruwan sha.
Shugaban karamar hukumar, Idowu Senbanjo, ta bayyana haka, ta km ace, shirin ya yi daidai da kudurin Majalisar Dinkin Duniya na muradun karni guda 6, wanda samar da tsaftaccen ruwan sha ga al’umma yana ciki.
- Gwamna Lawal Ya Raba Kayan Noma Ga Manoman Arewacin Zamfara
- Majalisa Ta Amince Tinubu Ya Ciwo Bashin Naira Tiriliyan 7.5
“Duk da haka rijiyar burtsatse da mutane da dama suka yi a sassan yankin Apapa amma ba a samun tsaftaccen ruwan sha, hakan kuma yake haifar da cututtuka daban-daban,” in ji ta.
Ta kuma kara da cewa, samar da ruwan ga al’umma ya samu ne da tallafin hukumar NPA.
“An yi watsi da aikin fiye da shekara 15 da suka wuce, aikin mai girma ne, muna godiya ga hukumar NPA da ta samar da kudaden da aka gudanar da aikin”. in ji ta
A nasa jawabin, shugaban kungiyar mazauna yankin Apapa, Austin Oyagha, ya bayyana godiyarsa ga karamar hukumar Apapa a bisa yadda ta hada hannu da NPA a ka samar musu da tsaftataccen ruwan sha.
“Mun yi sa’ar samun shigowar NPA a kan harkokin jin dadin yankinmu, bayan samar mana da tsaftataccen ruwa sun kuma gyara mana hanyar nan da ake kira Liverpool Road’, muna godiya ga shugaban Hukumar, Alhaji Mohammed Bello Koko a bisa wannan kokarin.