Wasu kamfanoni biyu na kasar Sin, sun baiwa wasu daliban makarantun firamare dake kasar Ghana kyauta, albarkacin bikin ranar yara ta duniya da aka shirya a birnin Jamestown, daya daga cikin al’ummomin da ke fama da talauci a Accra, babban birnin kasar Ghana.
Kamfanin CRCC Harbor da kamfanin CCCC First Harbor Consultants CO., LTD, sun ba da gudummawar gwomman kwallayen kafa, da jakunkuna na makaranta, da fensira masu launi, da abin goge rubuta, da sauran kayan makaranta masu yawa ga makarantar reno ta Chirst the king of kings, wadda ke kusa da tashar kamun kifi ta Jamestown da kasar Sin ta samar wanda kamfanonin biyu suka gina.
Shugaban makarantar Paul Yaw Owusu, ya yaba wa manyan kamfanonin kasar Sin da taimakon da suka baiwa makarantar ta hanyoyi daban-daban, kama daga bayar da gudumawa zuwa aikin tsaftace muhalli.
Ya bayyana cewa, ilimi shi ne mabudin samun nasara, kuma an san cewa, kayayyakin da kamfanonin suka samar, za su taimakawa yaran matuka a kokarinsu na samun ilimi, don zama abin da suke so su zama a nan gaba. (Ibrahim)