Ministan Ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya, Ambasada Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa, sakin matar Mohammed Bazoum da dansa da sojojin juyin Mulki suka yi a Nijar wani mataki ne mai ma’ana na maido da zaman lafiya a kasar da ma yankin baki daya.
Tuggar, wanda kuma ke rike da mukamin shugaban kwamitin sulhu da tsaro, ya yabawa majalisar tsaro ta kasar da ta sake su daga kullen gida tun bayan hambarar da gwamnatin Muhammadu Bazoum.
- Juyin Mulki: Faransa Ta Rufe Ofishin Jakadancinta Na Nijar
- Shugaban Mulkin Sojin Nijar Zai Mika Jadawalin Mulki Ga Farar Hula
Ya kuma sake yin kira ga gwamnatin karkashin jagorancin Janar Abdourahamane Tchiani da ta gaggauta sakin Mohammed Bazoum daga hannun ta.
Tuggar ya bukace su da su kyale Bazoum ya fita zuwa wata kasa, inda ya ce, hakan, zai zama wani muhimmin mataki na samar da damar ci gaba da tattaunawa kan dage takunkumi da aka kakaba wa kasar. Ya kara da cewa, hakan na da matukar muhimmanci ga samun walwala da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Nijar da ma yankin baki daya.