Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa(INEC) a Jihar Kano ta ce ta kammala dukkanin shirye-shiryen gudanar da zaben cike gurbi a kananan hukumomin Kunchi/Tsanyawa, Kura/Garin Malam da Rimin Gado/Tofa na majalisar dokoki da aka shirya gudanarwa a cikin watan Fabrairu.Â
Kwamishinan zaben jihar, Abdu Zango ne, ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi ga masu ruwa da tsaki a hedikwatar hukumar da ke Kano a ranar Talata.
- Da Dumi-dumi: Kotun Koli Ta Tanadi Ranar Yanke Hukunci Kan Shari’ar Kujerar Gwamnan Filato
- Kotu Ta Umarci Gwamnatin Tarayya Ta Biya Emefiele N100m Kan Tsare Shi Ba Bisa Ka’ida Ba.Â
“Mun shirya tsaf domin gudanar da zaben tare da kwararru wanda jami’an zabe a shirye suke su gudanar da sahihin zabe a kananan hukumomi shida na jihar.
“Za mu gudanar da zabe a rumfunan zabe 66 a fadin kananan hukumomin shida.
“Duk mutumin da ba shi da katin zabe ba zai yi zabe a kananan hukumomin ba,” in ji shi.
Ya ce tuni hukumar ta tura wasu muhimman kayayyaki ga daukacin kananan hukumomin da abin ya shafa.
Zango ya bayyana cewa za a yi amfani da na’urar BVAS a yayin sake gudanar da zaben da nufin tabbatar da sahihin zabe.
Ya kuma bayyana kwarin gwiwar kan gudanar da zaben cike gurbin.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Hussaini Gumel ya ce sun shirya samar da tsaro a dukkan harkokin zabe a kananan hukumomin da abin ya shafa.
Gumel wanda ya samu wakilcin CSP Hamma Abdullahi, ya ce ‘yan sanda za su tura jami’an tsaro kowace rumfar zabe domin bai wa mazauna kananan hukumomin shida.
Ya gargadi shugabannin jam’iyyun siyasa da za su shiga zaben da su ja hankalin magoya bayansu da su guji tada tarzoma.