Bisa kididdigar da hukumar kula da harkokin sakwanni ta kasar Sin ta fitar a yau Talata, an yi kiyasin cewa, a shekarar 2023, yawan kunshin sakwannin da aka aike da su a kasar ya kai biliyan 162 wanda ya karu da kashi 16.5 cikin dari, kuma kudin shigar da aka samu a bangaren ya kai triliyan 1.5, wato ya karu da kashi 13.5 cikin dari bisa makamancin lokacin a bara.
Daga ciki, yawan kunshin sakwanni da aka yi sufurinsu a cikin kasar ya kai biliyan 132 wanda ya karu da kashi 19.5 cikin dari, kuma kudin shigar da aka samu ya kai triliyan 1.2, karuwar kashi 14.5 cikin dari bisa makamancin lokacin a bara.
A cewar hukumar kula da harkokin sakwanni ta kasar Sin, a shekarar 2024, za ta inganta karfin aikin sufurin sakwanni bisa kammala hanyar sadarwa ta kasar, musamman ma ci gaba da kyautata yanar hukumomin kula da harkokin sakwanni a yankunan yamma da tsakiya na kasar, da karfafa daidaiton ci gaba, da kuma ba da gudummawarsa wajen gina babbar kasuwar bai daya ta kasar.(Safiyah Ma)