Masu Tafsiri sun yi sabani game da ma’anar aya ta 6 da ta 7 a cikin Fatiha, wato “Allah ka shiryar da mu hanya madaidaiciya. Hanyar wadanda ka yi ni’ima a gare su, ban da wadanda ka yi fushi da su (Yahudawa), ban da batattu (Nasara)”.
Malam Mawardi ya ruwaito cewa Abul Aliyati da Hasanul Basri sun ce ma’anar hanya madaidaiciya a wannan ayar tana nufin Manzon Allah (SAW) da zababbun Iyalan Gidansa da Sahabbansa (RA). Wato kullum Musulmi muna addu’ar Allah ya shiryar da mu hanyar Manzon Allah (SAW), bin sa, son sa da kuma riko da abin da ya zo da shi.
- 2027: Atiku, Kwankwaso Da Obi Na Shirin Kafa Babbar Jam’iyyar Adawa – Pat Utomi
- Kwamoti B Laori Ya Kaddamar Da Ajujuwa 3 A Mazabar Kodomti A Numan
Makkiy ya ruwaito har ila yau daga Abul Aliyati da Hasanul Basri irin wannan din. A ruwayarsa, hanya madaidaiciya ana nufi Manzon Allah (SAW) da Abokansa (Abubakar da Umar RA). Har ila yau, Abullaisu Samarkandi ya ruwaito irin wannan shi ma daga Abul Aliyati, ko da labarin hakan ya riski Hasanul Basri cewa ga abin da Abul Aliyati ya fada sai ya ce “Wallahi ya yi gaskiya kuma ya nasihantar da al’umma”. Imamul Mawardi ya ruwaito wannan shi ma a cikin Tafsirin ayar “Allah ka shiryar da mu hanya madaidaiciya” daga Abdulrahman bin Zaidin.
Abu Abdulrahmanus Sulamiy ya ruwaito daga sashen malamai cewa ayar cikin Suratul Bakra, “… duk wanda ya kafirce wa gumaka kuma ya yi Imani da Allah, to ya yi riko da igiya mai kwari”, wannan igiya mai kwarin tana nufin Annabi Muhammad (SAW).
Kila kuma an ce ma’anar igiya mai kwarin ana nufin Musulunci. Kila kuma an ce ana nufin shaidawar nan ta Tauhidi (La’ilaha illallah Muhammadur Rasulullah SAW).
Sahlu bin Abdullahi ya ce cikin fadin Allah (SWT) cewa “idan kun kirga ni’imomin Allah ba za ku iya kai karshenta ba”, wannan ni’imar ana nufin Annabi Muhammad (SAW). Wato idan za mu kirga ni’imomin da muka samu bisa samun Annabi (SAW) ba za mu iya kididdigewa har zuwa karshe ba. Shi ya sa ma idan ba a manta ba, mun yi bayani a kan yadda Allah ya yi mana gori da samun Annabi (SAW) a matsayin babbar baiwa.
Domin idan ba Annabi Muhammad (SAW) ba, ni’imomin da ake ganin ni’ima ne Allah ya bai wa makiyansa, idan kudi ne ko dukiya ko yawan ‘ya’ya ko mulki kila ma ya baiwa makiyan fiye da yadda ya baiwa masoya. Amma ni’imar samun Annabi (SAW) ko a cikin Musulmi ma ba kowa ba ne, musamman wadanda ke ganin idan ka girmama Annabi (SAW) ka so shi sosai, ka bi shi suke ganin kamar ka baude hanya.
Malaman da suka kawo mana bayanan nan na sama su ne gangariyar malamai magabata. Wasu a cikinsu Tabi’ai ne, wasu ma Sahabbai ne (RA).
Ayar nan ta cikin Suratuz Zumar, aya ta 33 da Allah (SWT) ya ce “Wannan da ya zo da gaskiya da wanda ya gaskata shi; su ne masu tsoron Allah”. Tulin masu Tafsiri sun tafi a kan cewa wanda ya zo da gaskiya shi ne Annabi Muhammad (SAW), wannan dama babu tantama. Wani sashe na malamai kuma suka ce ma’anar wanda ya gaskatan ma shi ne Annabi Muhammad (SAW), shi ya sa ma ake karanta harafin “dal’ na kalmar “sadaka’ da ke cikin ayar da wasalin sama kawai ba tare da sanya karfi (shidda) ba, wato a ce “sadaka” ba “saddaka” ba.
Malamai masu wannan fahimtar suka ce ayar cikin Bakra ta “Amanar rasuulu…”, ta nunar da cewa Annabi (SAW) shi ne wanda aka aiko da sakon Allah kuma shi ya fara yin imani da abin da aka aiko shi da shi, sannan daga bisani Muminai. Don haka sai ya zama shi ne wanda ya zo da gaskiya kuma ya gaskata gaskiyar da ya zo da ita.
Amma wasu masu Tafsirin kuma sun ce ma’anar “wanda suka gaskata shi’ ana nufin Muminai ne. Manzon Allah (SAW) ya zo da gaskiya Muminan al’ummarsa kuma suka gaskata shi. Wasu malaman kuma har ila yau sun ce, wanda ya zo da gaskiya shi ne Annabi Muhammad (SAW); wanda ya gaskata shi kuma ana nufin Sayyidina Abubakar (RA), har ma suka ce shi ya sa ake masa lakabi da “Assiddiyk”. Wasu kuma suka ce Sayyidina Aliyu (Karramallahu waj’hahu) ne ake nufi. Akwai wasu masu fahimtar kuma daban da wadannan da muka kawo.
Malam Mujahid ya ce a cikin fadin Allah (SWT) a Alkur’ani cewa “ku sani fa; da ambaton Allah ne zuciya take samun natsuwa”, ayar tana nufin “ambaton Annabi Muhammadu” ne (SAW). Shi ya sa Manyan Bayin Allah da an fada musu Annabi Muhammad (SAW) nan take sai su ji zuciyarsu ta natsu.
Allah ya kara natsar da zuciyoyinmu baki daya da Annabi Muhammad (SAW) zahirinsa da badininsa.
Allah Yana bayyana mana wasu daga cikin kyawawan halayen Manzon Allah (SAW) domin mu yi koyi. Yin hakan zai gyara mana rayuwarmu da zamantakewarmu a tsakaninmu da sauran al’ummomi wadanda ba Musumi ba. Har ila yau, wadannan halaye da za mu kawo bayaninsu a kasa, sinadarai ne na yiwa al’umma shugabanci nagari wanda ya kamata kowane shugaba ya yi koyi da su a cikin mulkinsa.
Allah Tabaraka wa Ta’ala ya fada a cikin Suratu Ali Imran cewa “saboda rahamar Allah ne ka yi sauki Gare su (sahabbansa), da ka zamanto mai tsanantawa; mai kaushin zuciya duk za su watse ba za su zo kusa da kai ba, ka dinga yi musu rangwame (idan suka yi ma abin da ya taba ka), ka nema musu gafara (idan sun saba wa Allah), ka rika yin shawara da su a cikin lamari – bayan an yi shawarar – idan aka yi niyyar aiwatarwa ka dogara da Allah, Allah yana son masu dogaro gare shi”.
Rangwamen da ake magana a kai a cikin ayar ba sau daya ake nufi ba, dauwama ake so a yi cikin yin ta. A bisa al’adar zamantakewar jama’a dole idan an zauna sai an saba, to idan an saba wa mutum ana so ya yi rangwame. Haka halin Manzon Allah (SAW) yake. Malamai sun ce wannan rangwamen tana nufin Kamar mutum ne ya yi bako yana cin abinci sai ya rika ce masa “ka ci malam”, ma’ana ai ba bakon ba ya cin abincin ba ne ya sa ake ce masa ya ci, ana ce masa haka ne don ya saki rai ya cigaba da cin abincin. Shi ya sa ma’anar “ka yi masu rangwamen” take nufin ka dauwama kana musu rangwame, ba sau daya ba kawai.
Shawara tana da matukar muhimmanci a cikin rayuwarmu. Manzon Allah (SAW) yana karbar wahayi ne daga Allah kan lamurransa. Amma sai gashi Allah ya umurce shi ya rika yin shawara da sahabbai cikin lamarinsa (SAW). Haka kuma ya rika gudanarwa, komai yana shawara da sahabbansa har ya ji wacce ta fi dacewa sai ya dauka ya yi amfani da ita.
Manzon Allah (SAW) ya ce “duk mai yin shawara ba zai yi nadama ba; sai dai bashi da sirri”.
Shawara tana da albarka, idan mutum yana yi zai rika ganin albarka cikin abubuwansa sai dai kuma zai kasance ba shi da sirri. Ba wai shawarar ce za ta gudanar da abu mai kyau ba, a’a, idan an tashi aikata abin da aka yi shawarar a kai, ana so a dogara ga Allah.
Ma’anar dogara ga Allah (Tawakkali) shi ne mutum ya bi sababin abin da yake son yi ko yake son aiwatarwa sai kuma ya mika wa Allah lamarin. Malamai sun ce ba a son rungume hannu a ki yin komai sai a ce an dogara da Allah (Tawaakuli).
Misali, idan mutum yana neman arziki to kar ya zauna, ya fita ya je wurin nema; kamar kasuwa ko ofis da sauransu kana sai ya dogara da Allah cikin abin da yake nema. Idan tsaron wani abu ne, ya sanya maigadi da abubuwan da suka kamata sannan ya ce ya dogara da Allah. Annabi (SAW) ya ce wa wani sahabi “daure dabbarka sannan ka dogara da Allah”.
Wannan Aya tana koyar da dukkanin sha’anin siyasa da mulki na al’umma. Maulanmu Shehu Ibrahim Inyass (RA) ya ce “duk shugaban da aka bashi ragamar mulkin al’umma idan ya yi amfani da wannan Aya, jama’arsa za ta kasance tare da shi, shi kuma zai amfanar da ita. Amma idan ya sanya tsanani a cikin mulkinsa, zai cuci jamarsa saboda kowa zai gudu ya bar shi”.
Akwai babban darasin da ya kamata mu koya daga wannan ayar na kiyaye dora wa jama’a mugun tsanani har su rasa inda za su sanya kansu. Manzon Allah (SAW) shi ne shugaban wannan al’ummar tamu amma bai tsananta mana ba, saboda rahamar Allah sai ya zamo mai taushin hali babu kausasawa. To idan har shugaban al’ummar baki daya zai kasance mau taushi, bai kamata wani da sunan malami a cikin al’ummar ya tsananta ma kansa kuma ya ce dole sai mutane sun bishi a kan hakan ba.
Dangane da darasin da za a koya daga wannan ayar da muka kawo a sama, Malam Samarkandi ya ce Allah ya tunatar da Sahabban Manzon Allah (da sauran al’ummarsa) cewa shi (SAW) mai jinkai ne ga muminai, mai tausayi ne gare su, mai taushin sasanni (yana da dadin zama, babu wanda zai ce yana jin tsoron zama da shi saboda wani halinsa). Da ya kasance mai kaushin zuciya, sahabbai za su watse babu wanda zai zo kusa da shi. Amma sai Allah ya sanya shi mai sauki da saukake abubuwa, da sakin fuska, da yawan yin alkhairi, mai taushin rai, kamar yadda Malam Dahhak ya fassara ayar.
Wannan aya tana karantar da mu girmaman halayen Shugaban Halitta Annabi Muhammad (SAW). Kowa ya dauke su ya yi koyi da shi (SAW), zai zama abokin kowa kuma shi ma zai so mutane.