Shugaban kasar Maldives Mohamed Muizzu ya ce, tun bayan da kasashen Maldives da Sin suka daddale huldar diplomasiyya a shekarar 1992, kasarsa ta samu goyon baya sau da dama daga kasar Sin. Musamman ma bayan da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar ziri daya da hanya daya, shekaru goma da suka wuce, yana mai cewa matsayin taimakawa juna da hadin gwiwa dake tsakanin kasashen biyu ya kai wani sabon mataki, inda yanzu huldar dake tsakanin sassan biyu ta riga ta kasance huldar sada zumunta ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni.
Mohamed Muizzu ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da wakilin CMG a baya-bayan nan.
- Me Ya Sa Duniya Ke Son Motocin Sin?
- Bankin Duniya Ya Yi Hasashen Bunkasar Tattalin Arzikin Nijeriya Da Kashi 3.3 A 2024
Shugaba Muizzu ya kara da cewa, shugaba Xi Jinping yana kaunar al’ummun kasarsa, kuma yana sanya su a gaban komai, dalili ke nan da ya sa shi samun karbuwa matuka daga wajensu, haka kuma tattalin arzikin kasar Sin ya samu ci gaba cikin sauri a karkashin jagorancinsa.
Da yake tsokaci kan shawarar raya duk duniya, da shawarar tabbatar da tsaro a fadin duniya, da shawarar wayewar kan duniya da kasar Sin ta gabatar, Mohammed Muizzu ya bayyana cewa, wadannan shawarwari suna da muhimamnci kwarai, kuma Maldives ta amince da su matuka. Ya ce shawarwarin za su taka rawa kan ci gaban daukacin bil Adama da duk duniya baki daya. A sa’i daya kuma, kasashen duniya za su amfana da karfin jagorancin kasar Sin cikin harkokin kasa da kasa.
Game da gadar sada zumunta ta Sin da Maldives da kamfanin kasar Sin ya gina a kasar, shugaba Muizzu ya ce, babban aikin gadar ya alamta dadadden zumuncin dake tsakanin kasashen biyu. Yana mai cewa, tun bayan kaddamar da gadar, ta sauya rayuwar dubban mutanen kasar Maldives, tare kuma da ingiza ci gaban tattalin arzikin kasar yadda ya kamata. (Mai fassara: Jamila)