Wata Kotun Majistare da ke Badagry a jihar Legas, a ranar Litinin ta bayar da umarnin tsare wasu mutane biyu, Sunday Adebayo, mai shekaru 31 da Kopo Sogbo, mai shekaru 41 saboda amsa laifin satar plantain da ayaba wanda kudinsu ya kai N10,000.
Alkalin kotun, Mista N. A. Layeni ne ya bayar da umarnin tsare su bayan sun amsa laifuka biyu da suka shafi aikata sata.
- Kotu Ta Daure Wani Dan Kasuwa Bisa Laifin Satar Kayan Kanti
- Kotu Ta Daure Wata Matashiya Kan Satar Katin Waya Na ₦275,400 A Kaduna
Layeni ya bayar da umarnin a tsare wadanda ake kara a gidan gyaran hali na Awhajigoh, Badagry.
Alkalin kotun ya dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 24 ga watan Janairu domin yanke hukunci.
Tun da farko, mai gabatar da kara, ASP Clement Okuoimose, ya shaida wa kotun cewa wadanda ake tuhumar sun aikata laifin ne a ranar 6 ga watan Janairu da misalin karfe 8:00 na safe a Estate Train Estate, unguwar Ilogbo Eremi a Legas.
Okuoimose ya ce wadanda ake tuhumar sun hada baki ne tare da aikata laifin sata.
Mai gabatar da kara ya ce wanda ake tuhumar ya saci tarin plantain da ayaba da kudinsu ya kai N10,000 mallakin mai karar, Alhaja Bilikisu.
Mai gabatar da kara ya ce laifukan sun ci karo da sashe na 411 da na 287 na dokar laifuka ta jihar Legas na shekarar 2015.