A jiya Lahadi, ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi, ya yi tsokaci kan yanayin da ake ciki a wasu shiyyoyi daban daban, a wani taron manema labaru da ya gudana a birnin Alkahira na kasar Masar, bayan da ya gana da takwaransa na kasar Masar Sameh Shoukry.
Dangane da rikicin da ake fama da shi a zirin Gaza, ministan na kasar Sin ya ce, rikicin na ta kara tsanani, lamarin da ya haddasa rasa rayukan dimbin fararen hula, da haifar da mummunan tasiri ga karin yankuna makwabta cikin matukar sauri. A cewar jami’in, kasar Sin a ko da yaushe tana goyon bayan ra’ayi mai dauke da adalci, inda take kokarin neman ganin a tsagaita bude wuta, a hadin gwiwarta da kasashen Larabawa, da na Musulmi, don kare fararen hula, da neman samun damar daidaita batun Falasdinu cikin adalci kuma daga tushe tun da wuri.
- CMG Ta Kammala Bitar Farko Ta Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Bana
- Ofishin Kula Da Harkokin Taiwan Na Majalisar Gudanarwa Da Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Sun Yi Tsokaci Kan Sakamakon Zabukan Taiwan
Sa’an nan, game da maganar tsaro da ta shafi bahar Maliya, jami’in Sin ya ce, kasar Sin tana damuwa da mai da cikakken hankali kan batun. Kana kasar ta yi kira da a dakatar da kai hari ga jiragen ruwa na fararen hula, don kare tsarin samar da kayayyaki da na cinikayya a duniya. A cewar Malam Wang, dalilin da ya sa ake samun tashin hankali a yankin bahar Maliya, shi ne habakar rikici daga zirin Gaza zuwa sauran wurare. Yanzu aikin da ya kamata a aiwatar da shi cikin gaggawa shi ne, a kwantar da kurar da ta tashi a Gaza, don magance ci gaban bazuwar rikicin.
Ban da haka, jami’in ya yi tsokaci kan yanayin da ake ciki a yankin Taiwan na kasar Sin. Ya ce, zaben da aka yi a yankin, aikin cikin gida ne na kasar Sin. Kana duk wani sakamakon da aka samu wajen zaben, ba zai canza hakikanin yanayin da ake ciki ba, wato kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, kana Taiwan wani yanki ne na kasar Sin. Kana ba zai girgiza ra’ayi na bai daya da gamayyar kasa da kasa ke da shi na kasancewar kasar Sin guda daya kawai ba.
Bugu da kari, Mr. Wang Yi wanda yake kai ziyara kasar Tunisia, ya bayyana sabon kwalejin nazarin harkokin diflomasiyyar kasa da kasa na Tunis, wato kwaleji daya tilo na harkokin diflomasiyya da aka kaddamar a yau Litinin, kuma Sin ta taimaka wajen ginawa a wata kasar Larabawa, a matsayin sabuwar alama ta dankon zumunta, kuma dandalin raya abotar Sin da Tunisia.
Wang Yi ya bayyana haka ne yau, lokacin da yake jawabi yayin bikin bude kwalejin a birnin Tunis. Bikin ya samu halartar shugaban kasar, Kais Saied da ministan harkokin wajen kasar, Nabil Ammar.
Wang Yi ya kuma yi kira da a yi kokarin inganta gina tsarin duniya mai daidaito tsakanin kasashen duniya da dama da dunkulewar tattalin arzikin duniya domin kowa ya amfana. (Bello Wang, Fa’iza Mustapha)