Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ta ce tana bukatar dala biliyan daya da miliyan 500 a shekarar 2024 domin ceto rayukan mutanen da ke cikin bukatar kulawar kiwon lafiya.
A cewarta daga cikin wadanda za ta ceto har da wadanda yakin Ukraine da kuma Gaza ya shafa.
A cewar sanarwar da shugaban WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya fitar, ya yi gargadin cewar kimanin mutane miliyan 300 ne a fadin duniya za su bukaci agajin kiwon lafiya a bana.
Ya ce daga cikinsu akwai kimanin mutane miliyan 87 da ke bukatar kulawar lafiya, don haka suke bukatar kudin da ya kai dala biliyan daya da miliyan 500 don gudanar da aikin.
Tedros, ya kuma yi tsokaci kan yadda matsalar sauyin yanayi ke kara ta’azzara, bayan tabbatar da shekarar da ta gabata a matsayin mafi zafi, lamarin da ya ce nada illa sosai ga lafiyar al’umma sannan ya haifar da fari a yankin Gabashin Afrika.
Shugaban, ya jaddada cewar da dama daga cikin wadanda ke cikin tsananin bukatar kulawar kiwon lafiya, galibi suna cikin yanayin neman dauki.
Tedros, ya ce kashi 12 na yawan kudin da hukumar ta bukata ne kadai ta iya samu a shekarar da ta gabata.