Da safiyar yau Talata 16 ga wata ne, firaministan kasar Sin Li Qiang ya isa cibiyar tarukan kasa da kasa dake birnin Davos na kasar Switzerland, don halartar taron shekara-shekara na dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya na bana, tare da gabatar da jawabi na musamman, inda ya jaddada cewa, Sin kasa ce mai cika alkawari, kana, zabar kasuwar kasar ba hadari ba ne, akasin haka, dama ce.
Jami’in ya ce, a ‘yan shekarun nan, Sin tana zama muhimmin karfi wajen samar da ci gaba ga duk duniya, da himmatuwa wajen zamanantar da kanta daga dukkan fannoni ta hanyar samar da ci gaba mai inganci, kuma tabbas tattalin arzikin kasar zai kara bunkasa yadda ya kamata. Ya ce, kasar Sin na da babbar kasuwa, kuma tana da bukatu sosai, al’amarin da zai samar da manyan damammaki ga habaka kasuwanci da zuba jari a duk duniya.
Firaministan ya ce, kasarsa za ta fadada bude kofarta ga kasashen waje, da maraba da kamfanonin kasashe daban-daban su zuba jari a kasar, da kara kokarin samar da wani kyakkyawan yanayin harkokin kasuwanci. (Murtala Zhang)