Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ce tun bayan rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayun 2023, tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari bai taba tsoma masa baki kan yadda yake jagoranci ba.Â
Tinubu, ya kuma kara da cewar, tsohon shugaban bai gabatar da ko da mutum guda ba domin nada shi a wani mukami a gwamnatinsa ba.
- Za A Rataye Mutane 2 Sakamakon Kashe Dan Acaba A Adamawa
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban Al’umma Da Wasu 12 A Taraba
Yayin da yake gabatar da jawabi wajen kaddamar da littafin da tsohon mai bai wa Buhari shawara a harkokin yada labarai Femi Adeshina ya rubuta, a kan yadda Buhari ya gudanar da mulkinsa.
Shugaba Tinubu, ya ce Buhari ya cika alkawarin da ya dauka na cewar zai zauna nesa da birnin Abuja, kuma ba zai sanya baki a mulkin da ke gudana ba.
Shugaban ya jinjina wa Buhari a kan hadin kan da suka kulla wajen ciyar da dimokuradiyya gaba.
Tinubu, ya ce idan ban da kiran da yake yi wa Buhari ta waya domin sanin halin da yake ciki da kuma gonarsa, babu wani abu da ke shiga tsakaninsu.
Kadan daga wadanda suka halarci kaddamar da littafin, sun hada da tsohon shugaban Nijeriya, Janar Yakubu Gowon da tsohon mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da ministocin da suka yi aiki tare da Buhari.