A ranar Juma’a kotun kolin Nijeriya ta sake tabbatar da nasarar zaben gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, da watsi da karar da dan takarar jam’iyyar PDP a zaben ranar 18 ga Maris, 2023, Mohammed Barde ya shigar gabanta.
Barde ya kalubalanci nasarar zaben Inuwa a kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar da kuma kotun daukaka kara har zuwa kotun koli.
- Kotun Ƙolin Nijeriya Ta Tabbatar Da Nasir Idris A Matsayin Gwamnan Jihar Kebbi
- Kotun Ƙolin Nijeriya Ta Tabbatar Da Zaɓen Sule A Matsayin Gwamnan Nasarawa
Duka kotunan uku sun tabbatar da Gwamna Inuwa a matsayin zababben gwamna jihar, inda hukuncin kotun ya bayyana Barde a matsayin wanda ba shi da hujja mai inganci wajen shigar da karar.
A kotun koli a karkashin jagorancin mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun ta tabbatar da hukuncin kotun daukaka kara.
LEADERSHIP ta rawaito cewa a ranar Alhamis kotun koli ta yi watsi da daukaka karar da jam’iyyar ADC da dan takararta Nafiu Bala suka shigar kan nasarar da Gwamna Inuwa ya samu a zaben 2023.
Jam’iyyar ADC da Bala sun sun kalubalanci nasarar zaben Inuwa dukda a sakamakon da suka samu na kuri’un da ba su gaza 2,000 a zaben ba.
Sai dai a karshe kotun ta kori karar da Nafiu Bala da jam’iyyarsa ta ADC suka shigar a sakamakon janye karar da lauyoyinsu suka yi.