Yana da matukar muhimmanci ga mai kiwon kajin gidan gona ya san yadda zai hada abincin kajinsa da kansa, musamman masu kiwon kajin gidan gonar masu saurin girma da ake kira a turanci ‘Broilers’.
Masara:
Abu na farko da mai kiwon kajin gidan gona zai fara tanada ita ce masara kamar kimanin kilo 50, sai a hada ta da abinci kajin da ya sayo kamar kilo 100 na buhu hudu ko kuma kilo 25 ga wanda zai hada buhu 2 kacal, amma ya danganta da yawan adadin da mai kiwon yake bukata wajen hada abincin.
- ‘Yan Bindiga Sanye Da Hijabi Sun Farmaki Ofishin ‘Yansanda A Katsina
- Kotun Ƙoli Ta Tabbatar Da Nasarar Zaɓen Gwamna Inuwa A Matsayin Gwamnan Gombe
Kazalika, zai iya samun adadin da ya yi daidai da kiyasin da ya ke bukata, wato kari daga kan kilo 50 zuwa sama ko kuma zuwa kasa da adadin da ya ke bukata, sai ya raba gida biyu ko kuma ya rubanya zuwa gida biyu.
Misali, abincin kajin buhu biyu; sai kuma masara kamar kilo 25 ko kuma buhu daya na abincin kajin, sannan kuma kilo 12.5 na masara.
Sai dai, ana son mai kiwon kajin ya tabbatar da ya auna adadin da yake bukata, wanda zai yi amfani da shi wajen ciyar da kajin.
Daga nan, sai ya kai wurin masu injin nika su nika masa daidai da yadda kajin za su ji dadin cin abincin.
Waken Soya:
Haka nan, wannan mai kiwon kaji zai tanadi waken suya kamar kilo 10 ga wanda zai hada buhu hudu kilo 100, kilo 5 ga mai hada buhu 2, kilo 2.5 ga mai hada buhu 1, amma ana bukatar waken ya kasance an nika shi kamar yadda aka yi bayanin na masara kafin a auna ko a hada da sauran kayan hadin, kafin a nika a soya shi kadan; don kone wadansu sinadarai da ke kawo rashin saurin narka abinci a cikin kaji.
Yanda za a soya shi kuma, a nan za a nemo yashi a zuba a cikin tukunya ko kwano babba, sai a dora a kan murhun girki a rika juyawa, bayan yashin ya dan yi zafi sai a zuba waken suyar a cikin tukunyar ko kuma a cikin babban kwanon, sai a rika juyawa akai-akai har zuwa dan wani lokaci, daga minti 5 zuwa 20.
Amma idan har bai soyu yadda ake bukata ba, ya danganta da yanayin yadda zafin wutar da aka rura ya ke. Sannan, ba a so mai suyar ya bari waken suyar ya kone da yawa, domin idan ya kone da yawa, babu wani amfani da zai yi; saboda za ta kai ga an kone sinadarin da yake da amfani a cikin abincin kajin, don haka idan za a yi suyar; ya kamata a lura sosai.
Kwakwar Manja:
Ana yin amfani da kwakwar manja wajen hada abincin kajin gidan gona, sannan ta na matukar taimaka wa kajin yadda ya kamata.
‘Palm Kernal Cake’:
A nan, idan abincin buhu 4 za a yi; sai a yi amfani da kilo 12 kadai, idan kuma buhu 2 ne da kilo 6 kawai za a yi amfani, idan kuma ga wanda zai yi buhu 1 ne; sai ya yi amfani da kilo 3 a hada wuri guda.
‘Oyster shell’:
Ana amfani da wannan ne, idan za a hada abinci da dusar ‘finisher’, domin yana dauke da sinadarin ‘calcium’ sosai, wanda ke sa wa kaji karfin yin kashi da kuma taimaka musu wajen samun karfin jiki da kafafunsu.
Ana so abincin da za a hada ya kai kimanin kilo 100, wato buhu hudu kenan; sannan ana amfani da kilo daya na ‘Oyster shell’, idan kuma buhu biyu ne kilo 0.5 za a saka, kilo 0.25 a buhu daya.
‘Bone meal ko fish meal’:
Ga wanda zai hada kilo 100, buhu 4 kenan zai yi amfani da guda 3 na ‘Bone meal ko fish meal’, wato a buhu 4 kenan, idan kuma kilo 50 ne buhu 2 za a yi amfani da kilo 1.5 0.75 ga wanda zai hada buhu a cikin kilo 1 ko kuma kilo 25.
Sindarin ‘Bitamins’ da na ‘Minerals Premid’:
Wannan shi kuma za a zuba kilo 0.25 a buhu 4, kilo 0.125 a buhu 2, 0.kilo 062 a buhu daya.
‘Methionine’:
Za a zuba kilo 0.3 a buhu 4 kilo 100 da kilo 0.15 a buhu 2, sai kilo 50 da kilo 0.75 a buhu daya na kilo 25.
Lysine:
Wannan shi kuma za a zuba kilo 0.25 a buhu 4, kilo 0.125 a buhu 2, 0 da kuma kilo 0625 a buhu daya.
Gishiri:
A nan ana amfani gishiri dan kadan ne, kamar kilo 0.2 a buhu 4 kilo 100, kilo 0.1 a buhu 2, kilo 50, kilo 0.05 a buhu daya kilo 25.
Gishiri na da matukar amfani a cikin sinadaran hada abincin kaji, domin idan ya yi karanci matsala ce, saboda mafi yawancin abincin kaji idan bai sa su girma ba, zai iya yiwuwa matsalar daga kamfanin da aka sarrafa abincin ne aka samu matsala wajen zuba gishiri.
Dalili kuwa a nan shi ne, gishiri na bude wa kaji ciki su ci abinci yadda ya kamata, kazalika kuma yana saita yanayin jikinsu tare da ba su kariya wajen halittu masu hadari a cikin kaji. Amma yana da kyau a kula idan gishirin ya yi yawa, yana kuma kawo matsaloli wadanda suka hada da mace-macen kajin.