Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, a ranar Asabar, 20 ga watan Janairu, ta karyata labarin karya na zargin satar mutane a rukunin gidajen River Park da ke Abuja.
Kakakin rundunar ‘yan sandan birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ce ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa, Nnandi Agu na Unguwar Games Village ya yi garkuwa da kansa a kokarin damfarar dan uwansa don karbar kudin fansa.
- Masu Garkuwa Sun Buƙaci A Biya Su Fansar Miliyan 30 Kan Mutanen Da Suka Sace A Abuja
- ‘Yan Bindiga Sun Harbe Dan Shekara 7 Bayan Garkuwa Da Mutum 10 A Abuja
Adeh, wanda ta tabbatar da cewa wanda ake zargin yana hannun ‘yan sanda, ya bayyana cewa, “Rundunar ‘yan sandan birnin tarayya Abuja tana sane da labarin da ake yada wa game da wani zargin yin garkuwa da mutane a River Park estate da safiyar yau (jiya) kuma tana son bayyana abunda ya faru sabanin rahotonnin da ake yada wa. Rahotanni sun ce, babu wanda aka yi garkuwa da shi a River Park Estate.”
Ta ci gaba da cewa, “Wani Nnandi Agu dan Games Village ne kawai ya kitsa labarin karya ya yi garkuwa da kansa a kokarin da yake na damfarar dan uwansa da ke zaune a rukunin gidajen. Wanda ake zargin a yanzu haka yana hannun ‘yan sanda yana amsa tambayoyi.”