ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, July 14, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Fasa Aure Bayan Sa Rana: Laifin Iyaye, Saurayi Ko Budurwa?

by Rabi'at Sidi Bala
2 years ago
Aure

LABARAI MASU NASABA

A Duba Halin Da Masu Buƙata Ta Musamman Ke Ciki

Falalar Goman Farko Na Zul-hajji 

Mun taba tattauna wannan batu a shafin da muke tattaunawa tare da tsokaci a kan al’amuran zamantakewa na Taskira. Amma saboda muhimmancinsa na ga ya dace na sake dawo da shi a wannan bangare na Marurun Zuciya, saboda wata matsala ce da har yanzu ake fama da ita a cikin al’ummarmu.

Wannan matsala da ke afkuwa ga wasu samarin, bayan kai kudi na gani ina so. Wasu daga cikinsu na daura damarar yin aure, wanda kuma har takan kai da an tura iyaye kai kudin na gani ina so, wanda hakan ke nuni da shaidar an bawa saurayi yarinyar da yake so bisa al’adar Malam Bahaushe.

  • Hadin Abincin Kajin Gidan Gona Masu Saurin Girma
  • Kotun Ƙoli Ta Sake Tabbatar Da Zaɓen Abiodun A Matsayin Gwamnan Ogun

Wanda kuma hakan ke sa a saka ranar auren masoyan zuwa tsahon wani lokaci. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, saka lokaci mai tsaho na aure kan janyo targarda na rugujewar yin auren ga wasu matasan.

Wanda bayan shudewar wasu lokuta da saka rana, iyayen yarinyar kan mayar da kudin auren ba tare da dalilin komai ba. A tawa fahimtar ana samun wannan matsalar ta kowanne bangare, ga su iyayen yarinyar da yarinyar har ma da shi kansa saurayin. Wasu iyayen yarinyar na zaba wa diyarsu namijin da za ta aura ta hangen abin da saurayi yake da shi, musamman wajen ganin yadda yake kashe wa diyarsu kudade masu yawa, yayin da suka samu wanda ya fi shi sai su yanke shawarar mayar wa da yaron kudinsa, musamman in muka yi duba da wannan zamani.

Wasu kuma ba haka bane, bunciken da suka yi ne akan saurayin tun a farko bai yiwu ba, sai bayan lokacin da aka saka ranar aure, sa’annan suke kara samun wasu bayanai a kan yaron, wanda suke ganin yarinyarsu sam! ba ta dace da tsarin yaron ko ahlin yaron ba. Yayin da wasu kuma ke kallon yawan dage-dagen auren da ake yi ke sawa su canja ra’ayinsu gudun kar yarinyarsu ta tsufa a gida. Wasu kuma ganin babu muhallin zama ko kadan ke sawa su fasa bawa yaron ko da kuwa yana da sana’ar yi. Wasu kuma rashin aikin yi da rashin muhalli ke sawa su fasa ba da diyarsu, Wasu kuma umarnin ‘Yarsu kawai suke bi, musamman in ta shiga babbar makaranta sai ta ga sam! ba ajinta ba ne, ko kuma idan ta sami wanda ya fishi sai ta nemi a fasa, su kuma iyayen ba sa duban ka da su zama kananun mutane idan suka maida kudin, amma a haka za su mayar gudun ka da su bata wa diyarsu rai.

Ta bangaren samarin kuwa wasu iyayen saurayin ke sa buri cikin auren wanda har takan kai a rasa lokacin gabatar da auren ko da kuwa an saka ranar auren, akan yawaita daga lokacin auren har ma ya zo ya wuce ba a yi ba, sakamakon burin da aka daukarwa bikin har zuwa lokacin bai gama tabbatuwa ba, har ta kai ga iyayen yarinyar sun gaji da jira sai su fasa. Wani saurayin kuma ya gina soyayyar ne bisa karya, abin da bai da shi ya nuna cewar yana da shi alhalin bai da komai, wani sa’in ma iyayen hayo su yake ba nasa ba ne, komai nasa na aro ne ya ki bayyana kansa a matsayin da yake da shi, wannan ya sa a duk lokacin da gaskiya ta bayyana sai iyayen yarinyar su fasa bawa yaron, domin ko kusa bai dace da diyar su ba.

Wani kuma saurayin yakan boye wasu dabi’unsa ne wanda su kansu iyayensa ba su san yana da dabi’un ba, musamman ta fannin addini ko wasu munanan dabi’un da basu dace da shi ba, a duk lokacin da iyayen yarinya suka gano hakan sukan fasa bawa saurayin diyarsu. Akwai abubuwa da dama wanda ke faruwa har takan ja a mayar da kudin na gani ina so, wanda wajen ya yi kadan a bayyana shi, sai dai a fade su a takaice. Ko shin laifin waye tsakanin Iyayen yarinyar, da yarinyar da shi saurayin? Ko me yake jawo hakan? Ta wacce hanya za a magance matsalar? Za ku iya aiko mana sakonninku ta wannan lamba: 09063836033

Aure
Rabi'at Sidi Bala
+ postsBio
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Fim ɗin ƙaddara: Anya Ana Samun Irin Wannan ƙaddarar Kuwa?
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Ko Kafa Ƴansandan Jihohi Zai Taimaka Wajen Kawo Ƙarshen Matsalolin Tsaro?
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Dalilan Da Suka Jawo Aka Ƙi Yin Maraba Da FIM House A Jihar Kano
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Zan Iya Auren Namiji Komai Talaucinsa Muddin Muna Son Junanmu -Maryam Labarina
ADVERTISEMENT

MASU ALAKA

A Duba Halin Da Masu Buƙata Ta Musamman Ke Ciki
Marurun Zuciya

A Duba Halin Da Masu Buƙata Ta Musamman Ke Ciki

June 20, 2026
Laifukan Intanet: Kotun Abuja Ta Karɓi Rahoton DSS, Ta Ba Da Belin Wani Ɗan Gwagwarmaya
Marurun Zuciya

Falalar Goman Farko Na Zul-hajji 

May 23, 2026
marayu
Marurun Zuciya

Bukatar Kulawa Da Marayu Da Masu Karamin Karfi

May 17, 2026
Next Post
An Cafke Mutumin Da Ya Kitsa Labarin Sace Kansa Don Karɓar Kuɗin Fansa Wurin Ɗan’uwansa

An Cafke Mutumin Da Ya Kitsa Labarin Sace Kansa Don Karɓar Kuɗin Fansa Wurin Ɗan'uwansa

LABARAI MASU NASABA

Abin Da Ake Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin” Da Aka Yanke Wa Sin Na Kashin Kanta Ba Shi Da Wani Amfani

Abin Da Ake Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin” Da Aka Yanke Wa Sin Na Kashin Kanta Ba Shi Da Wani Amfani

July 13, 2026
Tafiye-tafiyen Fasinjojin Jirgin Kasa A Kasar Sin Sun Haura Biliyan 2.3 A Rabin Farko Na Bana

Tafiye-tafiyen Fasinjojin Jirgin Kasa A Kasar Sin Sun Haura Biliyan 2.3 A Rabin Farko Na Bana

July 13, 2026
Gwamnatin Tarayya Za Ta Ƙaddamar Da Tsarin Daƙile Rugujewar Gine-Gine

Gwamnatin Tarayya Za Ta Ƙaddamar Da Tsarin Daƙile Rugujewar Gine-Gine

July 13, 2026
Me Ya Sa Ake Ganin Afrika Na Da Damar Taka Rawa A Tsarin Tattalin Arzikin Duniya?

Me Ya Sa Ake Ganin Afrika Na Da Damar Taka Rawa A Tsarin Tattalin Arzikin Duniya?

July 13, 2026
Jiragen Kasan Sin Sun Yi Tafiye-Tafiyen Fasinjoji Sama Da Biliyan 2.3 A Rabin Farko Na Bana

Jiragen Kasan Sin Sun Yi Tafiye-Tafiyen Fasinjoji Sama Da Biliyan 2.3 A Rabin Farko Na Bana

July 13, 2026
Kotu Ta Hana INEC Amincewa Da Tarukan ADC Ƙarƙashin Jagorancin David Mark

Kotu Ta Hana INEC Amincewa Da Tarukan ADC Ƙarƙashin Jagorancin David Mark

July 13, 2026
Majalisar Gudanarwa Ta Sin Ta Wallafa “Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-Biyar Karo Na 15 Kan Kiyaye Lafiyar Al’ummar Kasar”

Majalisar Gudanarwa Ta Sin Ta Wallafa “Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-Biyar Karo Na 15 Kan Kiyaye Lafiyar Al’ummar Kasar”

July 13, 2026
Xi Zai Halarci Bikin Bude Babban Taron AI Na Duniya Na 2026, Inda Zai Gabatar Da Muhimmin Jawabi

Xi Zai Halarci Bikin Bude Babban Taron AI Na Duniya Na 2026, Inda Zai Gabatar Da Muhimmin Jawabi

July 13, 2026
Sin Ta Fitar Da Rahoton “Sake Karyata Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

Sin Ta Fitar Da Rahoton “Sake Karyata Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

July 13, 2026
Firaministan Sin Ya Jagoranci Taron Nazarin Tattalin Arziki Tare Da Masana Da ‘Yan Kasuwa

Firaministan Sin Ya Jagoranci Taron Nazarin Tattalin Arziki Tare Da Masana Da ‘Yan Kasuwa

July 13, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.