Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci a yi iyakacin kokarin gano tare da ceto mutanen da suka bace a zaftarewar kasa da ta afku a gundumar Zhenxiong dake birnin Zhaotong na lardin Yunnan da ke kudu maso yammacin kasar Sin.
Xi, ya ba da umarnin ne bayan zaftarewar kasa da ta afku a gundumar a safiyar yau Litinin.
- Wakiliyar Musamman Ta Shugaban Kasar Sin Ta Halarci Bikin Rantsar Da Shugaban Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo
- Wang Yi: Sin Na Fatan Hade Dabarun Raya Kasa Da Jamaica
Mahukuntan yankin sun ce mutane 47 sun makale bayan da kasa ta zaftare ta binne gidajensu a safiyar ranar Litinin a birnin na Zhaotong.
Hukumomin kula da bala’o’i na lardin sun fara aikin ba da agajin gaggawa tare da tura masu aikin ceto da dimbin injunan kashe gobara da sauran kayayyakin aiki.
Fiye da mutane 200 ne aka kwashe cikin gaggawa daga yankin. (Yahaya)