Masu masaukin baki, Ivory Coast na dab da ficewa daga gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON) bayan da ta sha kashi da ci 4-0 a hannun Equatorial Guinea a wasansu na karshe a rukunin A a Abidjan ranar Litinin.
Emilio Nsue ne ya zura kwallaye biyu a ragar Ivory Coast kafin Pablo Ganet da Jannick Buyla su jefa nasu kwallayen.
Wannan rashin nasara ta sa Ivory Coast ta koma matsayi na uku, kuka take kan siradin ficewa daga gasar tun a matakin rukuni.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp