Ma’aikatar harkokin wajen Kasar Sudan ta sanar da cewa, gwamnatin kasar ta sake jaddada aniyarta ta kawo karshen rikice-rikice a kasar, da shimfida zaman lafiya a kasar baki daya. A sa’i daya kuma, ta jaddada cewa, ya kamata bangarorin biyu da rikicin ya shafa su aiwatar da “sanarwar Jeddah” da sauran harkokin da abin ya shafa da farko, domin a fara yunkurin shimfida zaman lafiya bisa dukkan fannoni.
Sanarwar ta nuna cewa, rundunar sojan RSF ta yi alkawarin aiwatar da “sanarwar Jeddah”, tare da janyewa daga birane da kauyuka da hukumomin gwamnati da ababen more rayuwar jama’a da kuma wuraren jama’a da ta mamaye, wannan shi ne matakin farko da da rundunar SAF ta gindaya wa sojojin kasar na yin shawarwari.
- Tinubu Ya Tafi Faransa Domin Yin Wata Ziyarar Sirri
- Kayan Da Aka Jigila Cikin Sauri A Sin Ya Alamta Babban Karfin Tattalin Arzikin Kasar
A ranar 15 ga watan Afrilu na shekarar 2023, rikicin ya barke a tsakanin rundunar RSF da rundunar sojan Sudan a Birnin Khartoum, fadar mulkin kasar. Daga bisani kuma ya bazu zuwa wasu wuraren kasar.
A ranar 11 ga watan Mayu na wannan shekara kuma, rundunar sojan Sudan da ta RSF suka kulla “Sanarwar Jeddah” a Birnin Jeddah dake Yammacin Kasar Saudiya, inda suka yi alkawarin tsaron fararen hula, tare da kauce wa duk wasu matakan sojan da za su kawo illa ga fararen hula. Tun daga wannan lokaci, bangarorin biyu sun sha kulla yarjejeniyar tsagaita bude wuta, amma, ba a aiwatar da su yadda ya kamata ba. A ranar 4 ga watan Disamba na shekarar 2023, Kasar Saudiya da sauran masu aikin shiga tsakani, sun ba da sanarwar cewa, za a dakatar da shawarwarin da bangarorin biyu suke yi a Birnin Jeddah.