Wata kotu a Saliyo ta tuhumi sojoji 27 da aikata laifuka kan zargin yunkurin kifar da gwamnati.
“Tuhume-tuhumen sun hada da yin bore da hana yin boren da taimaka wa makiya da wasu laifuka,” kamar yadda ma’aikatar tsaro ta fada cikin wata sanarwa.
- Gobara: Gwamnan Yobe Ya Bai Wa ‘Yan Kasuwar Waya Tallafin Miliyan 100
- Gwamnatin Tarayya Ta Kafa Kwamitin Sa ido Kan Tsaro A Hanyar Abuja Zuwa Kaduna
A watan Nuwamban bara, ‘yan bindiga suka far wa wani sansanin sojoji da wasu gidajen yari a Freetown, inda suka saki kusan fursunoni 2,000.
Hukumomi sun bayyana hakan a matsayin yunkurin kifar da gwamnati.
A makon da ya gabata ne aka tuhumi tsohon shugaban kasar Ernest Bai Koroma da cin amanar kasa.
Ya musanta hannu a tuhume-tuhumen da suka kai ga kashe mutum kusan 20.
Hukumomi suna kuma tuhumar daya daga cikin dogarin tsohon shugaban kasar tare da tsoffin ‘yansanda 11 da ma’aikatan gidan yari.
An yi zama kafin soma shari’ar sojojin 27 a wata kotu da ke Birnin Freetown. An kuma dage zaman zuwa gobe Laraba.
Tashin hankalin da aka yi a watan Nuwamba ya zo ne watanni biyar bayan zaben da Shugaba Julius Maada Bio ya sake lashewa karo na biyu.
Sai dai ‘yan hamayya sun yi watsi da sakamakon zaben inda masu sa ido kan zaben daga kasashen duniya suka soki zaben saboda rashin tabbatar da gaskiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp