Wakilin kasar Sin, ya bayyana a jiya Talata cewa, ba za a lamunci kin amincewar da shugaban kasar Isra’ila ya yi kan kafa kasashe guda biyu a matsayin mafita ba.
Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun ya bayyana cewa, samar da kasashe biyu, wato Falasdinu da Isra’ila, ita ce hanya daya tilo da za a iya tabbatar da zaman lafiya ga bangarorin 2, kuma wata babbar bukata ce ta aiwatar da kudurorin kwamitin sulhun MDD.
Zhang ya ci gaba da cewa, kasar Sin ta yi kira da a kara kaimi wajen gudanar da harkokin diflomasiyya, domin kiran taron kasa da kasa, da kaddamar da matakai masu ma’ana a tsakanin bangarori daban daban cikin sauri, ta yadda za a sake farfado da manufar siyasa ta neman kafa kasashe biyu. (Yahaya)