Hukumar Kare Hakkin Bil’adama (NHRC), ta ce matsin rayuwa ta sa magidanta 106 a Jihar Gombe sun yi watsi da kula da ‘ya’yansu a shekarar da ta wuce.
Jami’in watsa labarai na hukumar, Ali Alola-Alfinti, shi ne ya shaida hakan ga kamfanin dillacin labarai ta kasa a Gombe.
Ya Kamata Sin Da Faransa Su Ba Da Jagora Wajen Yin Mu’amala A Shekaru 60 Masu Zuwa
Kofin Afirka 2023: Yadda Manyan Kasashe Ke Tafka Abin Kunya
Ya nuna damuwa kan karuwar yasar da yara da ake samun yi a Jihar Gombe, inda ya ce, hukumar ta damu matuka da hakan.
Mista Alola-Alfinti, ya ce, cikin korafe-korafe 280 da suka amsa a 2023, guda 106 na watsar da yara ne, da ke nuni da kaso 37.9 cikin dari na korafe-korafen da suka sauma a cikin shekarar.
Ya ce, watsar da yara na samuwa ne sakamakon yadda iyaye ke kaurace wa nauyin da ke kawukansu.
Ya kara da cewa a lokacin da uba ya kasa samar da kulawar da ta dace wa ‘ya’yansa, hakan zai kai ga zaman yaron wanda aka yi watsi da shi da fita sha’aninsa, kuma hakan zai iya shafan kiwon lafiyarsa da ma ta kwakwawarsa.
Ya ce, “Magidancin da ya yi watsar da ‘ya’yansa da matansa ba tare da abinci ba, babu kulawa babu sauran abubuwan bukata na rayuwa, mun samu kesa-kesai guda 106 na yaran da aka yi watsi da lamarinsu a 2023, sakamakon matsin rayuwa, wanda shi ne kaso mafi tsoka da muka amsa.
“Babban dalilin da ke janyo faruwar wannan lamarin shi ne matsin tattalin arziki, iyaye da dama ana daura musu laifin ne sakamakon halayensu na ko-in-kula.”
Ya ce, yaran da aka watsar nauyi ne a kan al’umma su kula da su domin guje wa gurbacewar rayuwarsu balle su zo su zama abun damuwa ga al’umma. Inda ya yi bayanin cewa masu ruwa da tsaki ya dace su shawo kan wannan matsalar.
A cewarsa, hukumar NHRC za ta kara azama wajen wayar da kan jama’a tun daga matakin farko kan wannan lamarin domin ganin iyaye suna daukan nauyin da ke kawukansu da muhimmanci na kula da rayuwar ‘ya’yansu.