Kungiyar masu aiwatar da sana’ar sanyawa da cire kudi ta kasa POS wato Association Of Point Of Sales Users In Nijeriya, za ta fara aiki gadan-gadan a cikin wannan shekara da muke ciki domin tabbatar da ganin ta inganta sana’ar wajen tsaftacewa da hana duk wani abu da iya hana ruwa gudu ga masu sana’ar.
Mai magana da yawun kungiyar nan a kasa Alhaji Maina Abdullahi ne ya sanar da haka cikin wata ganawarsu da wakilin LEADERSHIP Hausa, inda ya ce, kungiya ce da dade tana shirya ayyuka a fadin kasar nan baki daya, a cewarsa kungiya ce da aka kafa ta domin samawa matasa aiki, kuma a halin yanzu hakar kungiya ya cimma ruwa duba da irin dinbin matasa da turuwa wajen shiga sana’ar ta POS, inda a cewarsa kwalliya tana biyan kudin sabulu, don haka a shirye suke da su fara aikin tsaftace sana’ar a wannan wata da za mu shiga, duba da irin korafe-korafen da ake samu na yawan cutar mutane da wasu bata gari ke yi a sana’ar.
- Ministan Harkokin Wajen Kasar Sin Zai Tattauna Da Mashawarcin Shugaban Amurka Kan Tsaro Yayin Ziyararsa A Thailand
- ‘Yan Bindiga Sanye Da Hijabi Sun Kashe ‘Yan Sanda 2 A Katsina
“Kungiya ce da aka kafa ta don ta kare hakkin masu sana’ar POS tare da kwato musu hakkokin nasu da kuma tsare musu dukiyoyinsu daga masu aikata laifuka na amundahana ko abin da ya yi kama da haka idan bukatar hakan ta taso, ta yadda zai zama ana gudanar da sana’ar ba tar da an cutar da wani ba,”in ji shi.
Ya ce, a halin yanzu kungiyar na ofisoshi 811 a fadin kasar nan, tare da abokan aiki 9,360.
“Kungiyarmu ta hana kai da manyan ofisoshi na gwamnati, da suka hada da jami’an tsaro da ofisoshin hada-hadar kudi domin ganin ta kare hakkin ‘ya’yanta,” a karshe ya yi kira ga dukkan masu sana’a POS da su ci gaba rike gaskiya da amana domin taimaka wa kungiyar wajen cimma nasarar gudanar da ayyukanta.