• English
  • Business News
Thursday, October 30, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Batura Kirar Sin Sun Jawo Hankalin Kamfanoni Daga Duk Fadin Duniya

by CGTN Hausa
2 years ago
Sin

“Babu wani kaya dake madadin kaya kirar kasar Sin”. Kwanan nan, kafar watsa labarai na Koriya ta Kudu, wato Korean Economy ya ba da rahoton matsalolin da kamfanonin kera motocin Koriya ta Kudu ke fuskanta dangane da wannan batu. 

Yayin da kasar Amurka ke ci gaba da kara takunkumi a kan kayayyakin da kasar Sin ke fitarwa ketare, kamfanonin motoci na Koriya ta Kudu da ke dogaro da kayayyakin batir na kasar Sin suna kokawa. Sakamakon haka, wadannan kamfanonin sun gabatar da ra’ayoyinsu na yin kira ga gwamnatin Amurka da ta sassauta abin da ake kira takunkumi kan kasar Sin, tare da ba su damar sayen muhimman kayayyakin batir daga kasar Sin.

  • Shugaba Xi Jinping Ya Mika Sakon Murnar Ranar Australia Ga Gwamna Janar Na Kasar
  • Shugaban Ghana Ya Kaddamar Da Sabuwar Matatar Man Fetur Da Sin Ta Gina A Kasar

A daya gefen duniya kuma, kamfanin Tesla na Amurka shi ma yana fuskantar irin wannan kalubale. Sakamakon dakushewar samar da batir na sabuwar motar lantarki ta Cybertruck, Tesla ya nemi tallafi cikin gaggawa daga masana’antun kasar Sin da fatan samun tallafin kayayyakin batir.

Daga kamfanonin Koriya ta Kudu zuwa kamfanonin Amurka, daga gwamnati zuwa ‘yan kasuwa, dukkansu sun aike da sako iri daya, wato ba za a iya samar da motoci masu aiki da sabbin makamashi ba tare da kasar Sin ba.

Bayanai na baya-bayan nan da ma’aikatar masana’antu da sadarwa ta kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, a shekarar 2023 yawan batir dake samar da makamashin lantarki da ake fitarwa a kasar Sin ya karu da kashi 87.1 cikin dari idan aka kwatanta da shekarar 2022, kuma girman kasuwar ya kasance a kan gaba a duniya tsawon shekaru bakwai a jere. Haka kuma, kamfanonin kasar Sin sun kai guda 6 a cikin manyan kamfanonin batir 10 da ke samar da batura ga motocin makamashin lantarki a duniya.

LABARAI MASU NASABA

Sin Za Ta Harba Kumbon Shenzhou-21

Xi Jinping: Sin Da Amurka Za Su Iya Hada Kai Don Sauke Nauyin Dake Wuyansu Na Manyan Kasashe Da Daukar Ainihin Matakai

Ci gaban masana’antar batir ta kasar Sin, ya sa kaimi ga bunkasuwar masana’antar kera motoci masu amfani da sabbin makamashi da karancin iskar carbon ta duniya. Wannan ya sa kokarin da wasu ‘yan siyasar Amurka ke yi don cire batir din kasar daga tsarin samar da motocin masu amfani da makamashin lantarki ba zai kai ga nasara ba. (Mai fassara: Yahaya)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin Za Ta Harba Kumbon Shenzhou-21
Daga Birnin Sin

Sin Za Ta Harba Kumbon Shenzhou-21

October 30, 2025
Xi Jinping: Sin Da Amurka Za Su Iya Hada Kai Don Sauke Nauyin Dake Wuyansu Na Manyan Kasashe Da Daukar Ainihin Matakai
Daga Birnin Sin

Xi Jinping: Sin Da Amurka Za Su Iya Hada Kai Don Sauke Nauyin Dake Wuyansu Na Manyan Kasashe Da Daukar Ainihin Matakai

October 30, 2025
Sakamakon Nazarin CGTN Ya Yabawa Gudunmuwar Sin Ga Dunkulewar Yankin Asiya Da Pasifik
Daga Birnin Sin

Sakamakon Nazarin CGTN Ya Yabawa Gudunmuwar Sin Ga Dunkulewar Yankin Asiya Da Pasifik

October 29, 2025
Next Post
Auren Gata : Gwamnatin Jihar Kebbi Ta Aurar Da Mata 300

Auren Gata : Gwamnatin Jihar Kebbi Ta Aurar Da Mata 300

LABARAI MASU NASABA

Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bernard Doro A Matsayin Ministan Harkokin Jin Ƙai

Yadda Ta Gudana A Taron Karɓar Ƴan Majalisa Shida Da Suka Koma APC

October 30, 2025
Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bernard Doro A Matsayin Ministan Harkokin Jin Ƙai

Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bernard Doro A Matsayin Ministan Harkokin Jin Ƙai

October 30, 2025
Wata 3 Da Naɗin Shugaban APC, Sunan Yilwatda Har Yanzu Na Nan A Matsayin Minista A Shafin Ma’aikatar

Wata 3 Da Naɗin Shugaban APC, Sunan Yilwatda Har Yanzu Na Nan A Matsayin Minista A Shafin Ma’aikatar

October 30, 2025
Tinubu Ya Nada Musa Aliyu A Matsayin Shugaban ICPC

Tinubu Ya Amince Da Ƙara Harajin Shigo Da Man Fetur Da Dizal Zuwa Kashi 15

October 30, 2025
Sin Za Ta Harba Kumbon Shenzhou-21

Sin Za Ta Harba Kumbon Shenzhou-21

October 30, 2025
Xi Jinping: Sin Da Amurka Za Su Iya Hada Kai Don Sauke Nauyin Dake Wuyansu Na Manyan Kasashe Da Daukar Ainihin Matakai

Xi Jinping: Sin Da Amurka Za Su Iya Hada Kai Don Sauke Nauyin Dake Wuyansu Na Manyan Kasashe Da Daukar Ainihin Matakai

October 30, 2025
Sojoji Sun Ceto Wani Mutum Da Aka Sace A Taraba

Sojoji Sun Ceto Wani Mutum Da Aka Sace A Taraba

October 30, 2025
Majalisar Dokokin Kano Ta Ce An Yi Rashin Adalci Wajen Ɗaukar Aikin Kwastam A Nijeriya

Majalisar Dokokin Kano Ta Ce An Yi Rashin Adalci Wajen Ɗaukar Aikin Kwastam A Nijeriya

October 30, 2025
Sin

Bai Kamata Gwamnati Ta Ke Ciyo Bashi Bayan Cire Tallafin Man Fetur Ba – Sanusi II

October 30, 2025
Tinubu Ya Gaza Wajen Magance Matsalar Tsaro A Nijeriya — Atiku

Atiku Ya Soki Gwamnatin Tinubu Kan Sauya Sunayen Waɗanda Aka Yi Wa Afuwa

October 30, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.