Babban lauya kuma mai rajin kare hakkin dan-Adam Femi Falana ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya mika kwarya-kwaryan kasafin kudi na Naira biliyan 200 da ake bukata na raya jami’o’in Nijeriya don kawo karshen yajin aikin ASUU.
Falana, na ganin wannan zai taimaka gaya wajen kawo karshen yajin aikin malaman jami’o’in, abin da ya tsayar da harkokinsu tun watan Fabrairu.
- 2023: APC Ta Yi Babban Kuskuren Hada Musulmi 2 Takara – Babachir
- Muna Kokarin Shawo Kan Wahalhalun Da Jama’a Ke Ciki – Buhari
Babban lauyan ya ce maganar da gwamnati ta yi cewa ba ta da kudin da kungiyar malaman jami’o’in kasar, ASUU ta bukata, ba magana ba ce, inda ya yi nuni da yadda gwamnatin ta shawo kan matsaloli irin na tallafin man fetur da kuma na bunkasa harkokin noma.
ASUU ta fara yajin aikin gargadi na mako hudu daga ranar 14 ga watan Fabrairu.
A ranar 14 ga watan Maris ta tsawaita shi da wata biyu domin gwamnati ta biya mata bukatunta, abin da bai samu ba.
Haka kuma ta kara zarcewa da mako 12, kamar yadda ta sanar ranar 9 ga watan Mayu.
Tun daga wannan lokaci kungiyar take yajin aiki, inda ta lashi takobin ci gaba da yi har sai gwamnati ta biya mata dukkanin bukatunta.
Bukatun da suka hada da, kyautata yanayin aikinsu da raya jami’o’in gwamnati da ba su ‘yancin cin gashin-kai da sauransu.
Wata babbar matsala daga cikin bukatun ita ce ta bayar da kudin farfado da jami’o’in wadanda suka kai kusan Naira biliyan dubu 1.1
Kudin da gwamnatin ta ce ba ta da shi tana mai nuni da faduwar farashin mai a lokacin wannan mulkin na shugaba Buhari.
Wata matsalar kuma ita ce ta amfani da tsari na musamman na biyan albashin malaman jami’o’in (IPPIS), wanda malaman suke da ja a kansa.