Wasu ‘yan bindiga a ranar Alhamis, sun kai kutsa fadar Olukoro na Koro da ke karamar hukumar Ekiti ta jihar Kwara inda suka kashe basaraken, Janar Segun Aremu (mai ritaya).
LEADERSHIP ta rawaito cewa ‘yan bindigar sun kuma yi awon gaba da matar sarkin da wasu mutane biyu.
- Karatun Al-ƙur’ani Da Hadda Ce Shi, Yana Taimawa Ginuwar Ƙwaƙwalwa -Gwamnan Kwara
- Gobara Ta Lalata Dukiyar Miliyoyin Naira A Kwara
Gwamnatin jihar ta tabbatar da kashe sarkin da sace matarsa da wasu mutane biyu.
Sanarwar da gwamnatin ta fitar da misalin karfe 10:42 na wannan dare ta ce: “Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya yi Allah wadai da kisan Olukoro na Koro a karamar hukumar Ekiti, Janar Segun Aremu.
“Mun samu rahoton wasu ‘yan bindiga sun kashe Sarki a cikin fadarsa a daren ranar Alhamis, sun kuma yi awon gaba da matarsa da wasu mutane biyu. Cewar sanarwar.
Gwamnatin jihar ta yi Allah-wadai da harin da kiran jama’a da a zauna lafiya, za kuma a dauki mataki kan hakan.