A gabannin bikin Bazara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai rangadin aiki a birnin Tianjin da ke arewacin kasar Sin, inda ya gana da jami’an kananan hukumomi da fararen hula.
A safiyar ranar 1 ga watan Faburairu, ya ziyarci kauyen Diliubu na garin Xinku na yankin Xiqing dake birnin, inda ya duba yadda ake farfado da aikin noma bayan aukuwar ambaliyar ruwa a shekarar bara, da ganawa da mazauna wurin da bala’in ya shafa. Da yamma kuma, ya je titin al’adun gargajiya dake birnin, inda ya duba yadda ake samar da kayayyaki a kasuwa a gabannin bikin Bazara, biki mafi muhimmanci ga al’ummar Sinawa, da kuma yadda ake kiyaye unguwar al’adu mai dogon tarihi. (Tasallah Yuan)